Wednesday, January 15
Shadow

Ana warkewa daga ciwon hanta

Ana warkewa daga mafi yawan cutar hanta da aka saba da ita a tsakanin al’umma saidai akwai kalar wadda ba’ warkewa daga ita saidai ai ta kokarin shan magani.

Yawanci ba’a cika ganin alamun cutar hanta ba, fara maganin cutar da wuri na da matukar amfani saboda idan hantar ta riga ta tabu, magani bai cika yin tasiri ba.

Akwai matakai 3 na ciwon hanta kamar haka:

Hepatitis: Wannan shine matakin farko da hanta ke fara kumbura saboda wata cuta data sameta ko kuma ta kasa yakar wata cuta data shigeta. Daga wannan matakine cutar ke tsallakawa zuwa matakin Fibrosis.

Fibrosis: A wannan matakine hanta zata fara tsotsewa tana kankancewa, jini zai daina zuwarwa hantar, sannan kuma iska ma zai daina zuwar mata yanda ya kamata kuma zata rasa sauran sinadarai masu amfani. A wannan matakine hantar ke samun illa sosai, saidai duk da haka a wannan mataki ana warkewa ta dawo daidai idan aka yi dace.

Karanta Wannan  Fitsarin rakumi yana maganin ciwon hanta

Cirrhosis: A wannan mataki, hantarka ta kurewa matsayin lalacewa, babu sauran sinadaran da zata iya aiki yanda ya kamata. Saidai duk da haka ana iya samun waraka a wannan mataki. Kuma ba lallai ka ga wata alama ba saboda jikinka na ta kokarin ganin ya magance matsalar.

Liver Failure: A wannan mataki, hantarka ta lalace gaba daya ba zata gyaruba saboda jikinka ya gaji da taimakawa wajan magance matsalar hantar. A wannan mataki ne idan ba’a canja maka ita ba, zaka iya mutuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *