Thursday, July 18
Shadow

Allah Sarki: Ji yanda auren wata mata ya mutu saboda kissar kishiya

Wata baiwa Allah da labarinta ke cike da ban tausai ta bayyana yanda aurenta ya mutu saboda kissar Kishiya.

Ta bayyana hakane a zauren yanar gizo na Arewa up.

Ga dai yanda labarin yake kamar yanda ta badashi:

Ta fara shimfida kamar haka:

yadda aure na ya mutu

assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh yadda aure na na biyu ya mutu a silar kissar kishiya a gaskiya maza idan kunsan Baku Isa da matanku na gida ba kudaina yinkurin Kara aure sbd ku kanku Baku Isa kuce ba bare Kuma mu da aka aura”

Ta ci gaba da bayar da labarin kamar haka:

“wallahi na fada Miki bansan me ya faru ba Kinga an kaini gidansa ranar Friday to Kuma Daman gaskiya kamar Yana tsoron matar tasa to kwana na uku muka fara rabon kwana to yaje yayi mata kwana 2 ya dawo yayimun kwana 2 ya koma gidanta to washegarin ranar sai naji shi shiru bezo yamun sallama ba to da farko nayi tunanin ko ya shigo Ina bacci me sai na duba time naga 11am sai nace to bari na kirashi naji lpy naji sa shiru sai yacemun wai Yana busy ya tafi kasuwa nace Masa to ba kayan Miya a gidan Kuma kaga yau Yan gidansu zasu zo sai cewa yayi shi ba ruwana na musu Mai da yaji nace Masa to da daddare ma najisa shiru Bai shigo sai washegari da asuba naji an bude gidan an shigo Ina fitowa na ganshi tare da matarsa wai kayansa yaxo diba nace Masa to sai ya shiga bedroom sai yace mata ta shigo ta dibi kayan suka shiga suka diba suka tafi sai nayi Masa text ta Whatsapp nace Masa me debe kayanka daga gidan Nan yake nufi be bayan Kuma yau zaka dawo gidan sai yace ay shi baze Kara kwana a gidan ba nace Masa dalili sai yayi shiru da daddare Daya dawo be shigo gidan ba sai ya kirani yace na leko sai na leka wai yazomun sallama ne sai da safe nace Masa to bayan ya tafi sai ya kirani yace na kunna data Dana bude data sai naga sakonsa wai kiyi hakuri na yimiki saki Daya tun da yamma nace Masa to Allah yasa Hakan yafi Alkhairi”

Karanta Wannan  'Ana samun ƙaruwar bautar da ƙananan yara a Najeriya'

Da yawa sun tausaya mata bayan jin labarin inda suka mata fatan Allah yasa haka ne mafi Alheri a gareta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *