
An yi janaʼizar matashi Ismaʼil Makaye da ke sanaʼar sayar da kayan kwalliya a unguwar Hotoro Tishama rasuwa, bayan ya rasu a gidan budurwarsa fitacciyar ƴar rawar Solon nan kuma ƴar TikTok Fati Cele.
Daya daga makusantansa ya shaida wa Arewa Updates cewa, Cele ce ta fito daga cikin gidanta da safiyar Jumuʼa tana ihun gobara, kuma ko da aka shiga an tarar da shi ya ƙone kuma da alamun jini a jikinsa.
Ya ce, ƴan sandan Dorayi Babba na tsare da Cele yayin da su ke ci gaba da bincike.
Abokanansa da ƙawayenta sun ce, dama a baya sun samu saɓani tsakaninsu har ta kai sun rabu kafin a baya-bayan nan su sake daidaitawa.

Fati Cele dai ƴar asalin jihar Borno ce da ke haya a unguwar ta Danbare, inda ta ke wasan Solo a wani gidan Gala da ke unguwar Sabon Garin Kano.
Makusancin nasa, ya ce, an kai shi asibitin Nassarawa kafin daga bisani a yi janaʼizarsa a unguwarsu wato Unguwa Uku ƴan awaki.
Tuni abokai da ƙawayensu ke ci gaba da bayyana alhini a dandalin TikTok tare da kiraye-kirayen a yi bincike a kan rasuwarsa.
Fati Cele na da mabiya dubu 32,500 a TikTok.