Monday, October 12
Shadow

Ana zargin daya daga cikin yaran Farfesa Isa Ali Pantami da wallafa cewa idan me gidansu ya ci zabe zai hana Maulidi a jihar Gombe

Ana zargin Daya daga cikin manyan yaran dan takarar Gwamnan jihar Gombe, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami, watau Abba Pantami da yin wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya rubuta cewa, Idan Pantami ya ci zaben gwamnan jihar Gombe zai hana Maulidi.

Screenshot na rubutun nasa yana ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake ta sharhi akai.

Inda a shafin Tauraron fina-finan Hausa Baba Sadiq aka fara ganin screenshot din wanda daga baya ya ci gaba da yaduwa.

Zuwa yanzu dai Abba Pantami bai ce komai kan lamarin ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: A karin farko tun bayan da aka ce cutar shanyewar rabin jiki ta kamashi, An ga Ministan Kudi a Birnin Landan tsaye da kafafunsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *