
Datti Baba Ahmad wanda dan takarar mataimakin shugaban kasa ne a jam’iyyar Labour party a shekarar 2023 ya bayyana cewa, jam’iyyar APC ce ta kawo matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Yace APC ce ta kawo matsalar tsaro a kokarin kawar da gwamnatin Tsohon shugaban kasa Jonathan.
Yace wannan martanine maganar da El-Rufai yayi kan matsalar tsaro.