
Jam’iyyar APC, ta yi zargin cewa, Wasu ‘yan Adawa ne ke daukar nauyin ‘yan Bindigar dake kai munanan hare-hare a fadin Najeriya dan a karya lagon Gwanatin shugaba Tinubu.
Hakan ya fito ne daga bakin daya daga cikin masu ruwa da tsaki na APC a jihar Osun, retired Brig.- Gen. Bashir Adewinbi.
Saidai yace shugaba Tinubu ya tashi tsaye haikan yana kokarin magance wannan matsala.
Ya bayyana hakane yayin wata ziyara da mata ‘yan APC suka kai masa.
Yace gwamnatin Tinubu na son amfani da makamai na zamani dan magance matsalar tsaron da ake fama da ita.