Babban shagon siyayya na Shoprite zasu kulle daya daga cikin rassansu dake babban birnin tarayya, Abuja saboda matsin tattalin arziki.
Wakilin kamfanonin, Dr Folakemi Fadahunsi ya tabbatar da hakan.
Sanarwar tace matsin tattalin arziki ne zai sa su kulle daga ranar 30 ga watan Yuni reshen dake Wuse Zone 5.
A baya dai, Shoprite sun kulle rassansu dake Kano i da shima suka bada uzurin rashin ciniki.