Wednesday, February 25
Shadow

Ashe Kwankwaso bai samu ganin Shugaba Tinubu a zuwan da yayi Villa, Ji yanda ta kasance

Rahotanni sun tabbatar da cewa, zuwa na karshe da Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi zuwa fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai samu ganin shugaban kasar ba.

An ruwaito cewa Kwankwaso da shugaba Tinubu sun gana ranar Litinin din data gabata.

Saidai Rahoton Daily Trust yace ba’a yi ganawa tsakanin Tinubu da Kwankwaso ba.

Daily Trust tace wani taro ne ya kai Kwankwaso fadar shugaban kasar amma ba ganawa da Tinubu ba.

Daily Trust ta kara da cewa majiyoyi na kusa da shugaban kasar sun tabbatar mata da cewa babu wata ganawa da aka yi tsakanin shugaba Tinubu da Kwankwaso.

Karanta Wannan  Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *