Saturday, January 4
Shadow

Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello Zaria dake jihar Kaduna zai fara aikin dashen koda ga marasa lafiya.

Hakan zai kawowa mutane sauki matuka wajan yin dashen kodar.

Daraktan kula da lafiya na jami’ar, Prof. Ahmed Umdagas ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi, yace tsakanin nan da watan Maris ne za’a fara aikin dashen kodar.

Yace mafi yawan kayan aikin da ake bukata suna kasa kuma ma’aikatansu an horas dasu kan yanda zasu gudanar da aikin.

Ya kuma bayyana cewa suna kokarin kawo kayan aikin kula da masu cutar daji watau Cancer.

Karanta Wannan  Shekararsa 70 Amma Aikinsa Shine Baiwa Masu Gaŕkuwa Da Mutane Bayanan Sirri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *