Friday, December 5
Shadow

Atiku Abubakar yayi magana kan rade-radin da ake cewa, ya baiwa Soja, AM. Yerima dankareriyar motar Alfarma

Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumunta cewa, Wai tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya baiwa sojan ruwa da suka kara da Wike, A. Yerima dankareriyar motar Alfarma.

Saidai a sanarwar da ya fitar ta bakin magana da yawunsa, Paul Ibe, Atiku Abubakar yace ba gaskiya bane be baiwa AM. Yerima kyautar mota ba.

Yace labarin karyane kuma yana kira ga mutane su yi watsi dashi.

An dai rika yada cewa Atiku Abubakar ya baiwa sojan ruwan, AM. Yerima kyautar motar Toyota SUV.

Karanta Wannan  Hotuna: Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *