Saturday, December 21
Shadow

Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo komabaya ga harkar ilimi a Najeriya

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin “zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi” inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa’idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi.

Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Za mu kubutar da dukkanin ƴan Najeriyar da ke hannun masu gârkụwą da mutane, inji shugaban ƴansanda na ƙasa IGP Egbetokun

Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa da kuma ɓata tsarin gwamnati.

Atiku ya ce, ‘Wannan sabon tsari na gwamnati ba zai yi tanadi ga dalibai masu hazaƙa ba wanda hakan ke nuna rashin mutunta hazaƙar ilimi.”

“Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen zaƙulo ɗalibai masu hazaƙa tare da tallafa musu, ba tare da la’akari da shekarunsu ba” Atiku ya kara da cewa.

Atiku ya buƙaci da a bar wa gwamnatocin jahohi kula da harkokin ilimi, wanda a tunaninsa zai fi dacewa da yadda ake yi a ƙasashen duniya.

Karanta Wannan  Yanzu Yanzu Gobara ta tashi a kasuwar kantin kwari (Thaiba General Enterprise LTD)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *