
A yau ne attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ke cika shekaru 68 da Haihuwa.
An haifi Dangote a ranar April 10, 1957 a garin Kano.
Mahaifiyarsa Mariya Sanusi Dantata jikace a wajen Attajirin dan kasuwa, Alhassan Dantata.
Mahaifinsa, Mohammed Dangote abokin kasuwancin Alhassan Dantata ne.
Dangote yayi karatu a jami’ar Al-Azhar ta birnin Cairo na kasar Egypt.
Bayan nan ne ya fara yiwa kawunsa Abdulkadir Sanusi Dantata aiki inda daga baya ya karbi bashin $3000 yana da shekaru 21 ya fara kasuwanci.
Dangote yace tun yana makarantar Firamare ya fara kasuwanci.