Monday, April 21
Shadow

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya cika shekaru 68 a yau

A yau ne attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ke cika shekaru 68 da Haihuwa.

An haifi Dangote a ranar April 10, 1957 a garin Kano.

Mahaifiyarsa Mariya Sanusi Dantata jikace a wajen Attajirin dan kasuwa, Alhassan Dantata.

Mahaifinsa, Mohammed Dangote abokin kasuwancin Alhassan Dantata ne.

Dangote yayi karatu a jami’ar Al-Azhar ta birnin Cairo na kasar Egypt.

Bayan nan ne ya fara yiwa kawunsa Abdulkadir Sanusi Dantata aiki inda daga baya ya karbi bashin $3000 yana da shekaru 21 ya fara kasuwanci.

Dangote yace tun yana makarantar Firamare ya fara kasuwanci.

Karanta Wannan  NNPCL ya fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *