Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Jam’iyyar Adawa ta kayar da shugaban kasa me ci a kasar Malawi, kuma ya amince da shan kaye

Jam’iyyar Adawa ta kayar da shugaban kasa me ci a kasar Malawi, kuma ya amince da shan kaye

Duk Labarai
Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya amince da shan kaye bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Laraba. Ɗantakarar adawa Arthur Peter Mutharika na jam'iyyar Democratic Progressive Party ne ya lashe zaɓen. "Sakamakon zaɓen ya nuna ƙarara cewa babban abokin adawata Farfesa Mutharika ya samu ƙuri'u mafiya yawa. Saboda haka, na kira Mutharika domin taya shi murna kan nasarar da ya samu," in ji shugaban cikin wani jawabi da ya yi 'yan mintuna da suka wuce. Ana sa ran hukumar zaɓe Malawi Electoral Commission za ta sanar da nasarar tasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha Alwashin daukar mataki akan Malam Lawan Triumph bayan da aka kai masa korafi akan kalaman da yayi kan Janabin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha Alwashin daukar mataki akan Malam Lawan Triumph bayan da aka kai masa korafi akan kalaman da yayi kan Janabin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Duk Labarai
Wasu mazauna birnin Kano a arewacin Najeriya sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW). Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi. A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa haihuwar Annabi da kaciya, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce saboda "ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciyar". A cewar malamin, karama na nufin "wani abin al'ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai". Kazalika, malamin ya ce ruwayoyin ba su inganta ba. Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin da su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta h...
Kalli Yanda Magoya bayan Shugaban kasar Kamaru ke yakin neman zabe da hotonsa ba tare da halarci wajan yakin neman zabenba

Kalli Yanda Magoya bayan Shugaban kasar Kamaru ke yakin neman zabe da hotonsa ba tare da halarci wajan yakin neman zabenba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, Magoya bayan shugaban kasar, Paul Biya na yakin neman zabe da hotonsa ba tare da shi ya halarci wajan yakin neman zaben ba. Paul Biya me shekaru 92 a Duniya ya sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zaben shugaban kasa da za'a gudanar nan da watan Oktoba. Biya a yanzu shine shugaban kasa mafi tsufa a Duniya kuma shine na biyu wanda yafi dadewa akan kujerar mulki a nahiyar Afrika. Rahotanni sunce ana ta yama didin bashi da lafiyane shiyasa ya kasa halartar wajan yakin neman zaben. Paul Biya dai ya sha fita zuwa kasashen waje wajan neman lafiya. https://www.youtube.com/watch?v=-BshD_B03uI?si=DrUIRfvLkCtkH0Jg
Idan na zama shugaban kasa, Yarbawa san fi baiwa mukami ba Hausawa ko Fulani ba>>Atiku Abubakar

Idan na zama shugaban kasa, Yarbawa san fi baiwa mukami ba Hausawa ko Fulani ba>>Atiku Abubakar

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, ba kamar yanda ake yada jita-jita ba wai Hausawa da Fulanine zasu fi rike manyan mukamai a gwamnatinsa ba, Yarbawa zai fi baiwa mukamai. Atiku ya bayyana cewa, Matarsa ta Farko, Bayarbiyace kuma suna da 'ya'ya 4 da ita. Yace Yarbawa na da matsayin na kusanci irin na 'yan uwantaka a wajansa. Hakanan yace yana girmamasu sosai, kamar yanda kafar voicenews.com.ng ta ruwaito
Kundin Adana Ababen Tarihi na Duniya ya cewa ‘yar Najeriya dake shirin yin Alfasha da maza 100 a rana daya dan ta shiga cikin tarihi cewa baya ta’ammuli da ayyukan Alfasha

Kundin Adana Ababen Tarihi na Duniya ya cewa ‘yar Najeriya dake shirin yin Alfasha da maza 100 a rana daya dan ta shiga cikin tarihi cewa baya ta’ammuli da ayyukan Alfasha

Duk Labarai
Hukumar kundin Adana Ababen Tarihi ta Duniya, World Guinness Record sun baiwa 'yar Najeriya, Ayomiposi Oluwadahunsi amsa game da aniyarta ta son yin lalata da maza 100 dan ta shiga kundin Tarihin amsa. Sun ce mata basa ta'ammuli da ayyukan alfasha. A baya dai tace zata aikata wannan abin Alfashanne a Ikorodu dake Legas nan da watan October. Maganar tata dai ta jawo cece-kuce sosai inda Guinness World Records suka bayar da amsa.
Kalli Bidiyo inda Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam ta bayar da labarin cewa, tun tana karamar yarinya ita kyakkyawace aka samu wani yayi Alfasha da ita ya làalata mata rayuwa

Kalli Bidiyo inda Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam ta bayar da labarin cewa, tun tana karamar yarinya ita kyakkyawace aka samu wani yayi Alfasha da ita ya làalata mata rayuwa

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Maryam Ta bayar da labarin yanda wani mutum ya lalata mata rayuwa tun tana karamar yarinya. Saidai da yawa sun ce bai kamata ta bayar da wannan labarin ba. https://www.tiktok.com/@shusaab/video/7551756706775190791?_t=ZS-8zzdiRonEP3&_r=1
Bana nufin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) gajiyayye ne, inji Malam Abdulrahman Umar bayan da kalamansa na cewa idan An kira Annabi da neman biyan bukata baya ji suka jawo cece-kuce

Bana nufin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) gajiyayye ne, inji Malam Abdulrahman Umar bayan da kalamansa na cewa idan An kira Annabi da neman biyan bukata baya ji suka jawo cece-kuce

Duk Labarai
Malam Abdulrahman Umar ya fito yayi karin haske game da kalamansa da suka jawo cece inda yace idan An je Saudiyya an kira Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) baya ji. Malam yace ba yana nufin nuna gajiyawa ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) bane. Saidai yace idan dai sallama ce ko salati Akawa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yana amsawa. Yace amma indai neman biyan bukata ne Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) baya ji. https://www.tiktok.com/@maigidansama0/video/7552961830906334480?_t=ZS-8zzc0xCVAYr&_r=1
Wata Sabuwar kungiyar gamayyar ‘yan Adawa me suna AGOBI 27 sun nemi Atiku ya hakura ya barwa Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027

Wata Sabuwar kungiyar gamayyar ‘yan Adawa me suna AGOBI 27 sun nemi Atiku ya hakura ya barwa Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027

Duk Labarai
Wata sabuwar kungiya me suna AGOBI 27 wadda gamayyar 'yan adawa daga jam'iyyun (SDMA), da ADC da wasu kungiyoyin fafutuka suka kafa, ta roki tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya hakura da takarar shugaban kasa a 2027 ya barwa Peter Obi. Kungiyar tace idan Atiku ya yadda da hakan, babu yanda Tinubu zai iya sake cin zabe a 2027. Tace amma idan aka kasa samun wannan matsaya, lallai Tinubu ne zai sake cin zabe dan kuwa ya shirya hakan tsaf. Kungiyar tace Atiku idan ya yadda da wannan kira, zai kasance wanda za'a rika tunawa dashi a tarihin Najeriya a matsayin wanda ya sadaukar da son ransa dan Najeriya ta ci gaba. Amma idan yace ba haka ba, ya bar Tinubu ya sake cin zabe, zai kasance wanda za'a rika tunawa a matsayin wanda ya biyewa son zuciyarsa maimakon ci ga...
Dangote ya bayyana jihohin da zai fara kai dakon man fetur kyauta da motocin tankokinsa

Dangote ya bayyana jihohin da zai fara kai dakon man fetur kyauta da motocin tankokinsa

Duk Labarai
Matatar Man fetur ta Dangote ta bayyana jihihin da zata fara kai dakon man fetur kyauta a Najeriya. Matatar ta bayyana jihihin ne a matsayin na farko kamin ta fadada jigilar man fetur din zuwa fadin Najeriya baki daya. Dangote ya shigo da tankokin man fetur wanda yace zai rika kaiwa gidajen mai man fetur dinsa kyauta wanda hakan ya jawo cece-kuce tsakaninsa da kungiyar tankokin.