Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan dalilin da yasa ba’a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a taron kasashen Duniya a kasar Japan

Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan dalilin da yasa ba’a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a taron kasashen Duniya a kasar Japan

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Dalilin da yasa ba'a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a wajan taron ci gaban kasashen Afrika a kasar Japan ba, wakilan Najeriya sai ranar Alhamis zasu isa wajan. Rahotanni sun watsu cewa, babu wakilin Najeriya a wajan inda sai wani dan Najeriya ne da ya halarci taron kuma abin bai masa dadi ba ya gabatar da kansa a matsayin shine ke wakiltar kasar. Saidai a bayanin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya halarci wajan taron, Bankin masana'antu, Bank of industry ya halarci wajan taron, Ministan wuta, da sauran manyan ma'ikatan gwamnati duk dun halarci wajan taron amma duk suna can suna ganawa da wakilan kasuwanci da zai amfani Najeriya. Ya kara da cewa, wadanda zasu tsaya a wajan da ak...
Da Duminsa: Bayan Kiraye-Kiraye, Gwamnatin Tarayya ta saka Asibitin Aminu Kano cikin wadanda aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Da Duminsa: Bayan Kiraye-Kiraye, Gwamnatin Tarayya ta saka Asibitin Aminu Kano cikin wadanda aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Duk Labarai
Zuwa yanzu dai an saka Asibitin Malam Aminu Kano dake Kano cikin asibitocin gwamnatin tarayya ta aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira dubu 12. A baya dai an samu suka ga gwamnati bayan data sanar da ragin kudin wankin kodar a asibitocin Gwamnatin tarayya ba tare da hadawa da asibitin malam Aminu Kano ba. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai musamman a kafafen sada zumunta. Saidai a cewar tsohon Hadimin Gwamnan Kano, Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana cewa, yanzu an saka Asibitin malam Aminu Kano cikin wadanda akawa ragin.
DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur’ani ta Duniya

DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur’ani ta Duniya

Duk Labarai
Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur'ani ta Duniya Bukhari Sunusi Idris ɗan asalin jihar Kano da ya wakilci Nijeriya gasar Musabaƙar Al-ƙur'ani ta duniya, ya samu nasarar zuwa mataki na uku, a ɓangaren Izu Sittin da Tafsir. Hakazalika ya samu kyautar Riyal dubu 400, wanda ya kai kwatankwacin Naira Miliyan 160. Gasar wadda aka gudanar a kasar Saudiyya. Wane fata kuke masa?
Kalli Hotunan dan Peter Obi da ake rade-radin dan Lùwàdì ne

Kalli Hotunan dan Peter Obi da ake rade-radin dan Lùwàdì ne

Duk Labarai
Hotunan dan Peter Obi me suna Oseloka Obi sun bayyana a kafafen sadarwa inda ake ta rade-radin cewa dan Luwadi ne. Oseloka Obi na zaunene a kasar Ingila kuma dan fim ne. IWasu magoya bayan Peter Obi na cewa ba gaskiya bane saboda Oseloka Obi dan fim ne kuma hotunan da akw yadawa ba na gaskiya bane. Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga Oseloka Obi ta tabbatarwa ko karyata wannan ikirari.
Albashin Dubu saba’in da bakwai da Gwamnatin Najeriya ke biya, ya yi kadan, ba zai fitar da ‘yan kasar daga Talauci ba>>Inji Kasar Amurka

Albashin Dubu saba’in da bakwai da Gwamnatin Najeriya ke biya, ya yi kadan, ba zai fitar da ‘yan kasar daga Talauci ba>>Inji Kasar Amurka

Duk Labarai
Kasar Amurka ta bayyana cewa, Albashin Naira 77,000 da Gwamnatin Najeriya ke biya yayi kadan, ba zai fitar da 'yan kasar daga Talauci ba. Amurkar ta bayyana hakane a wani rahoto data fitar. Tace duk da gwamnatin tarayya ta nunka Albashin da ake biya a baya amma hakan yayi kadan matuka ya fitar da 'yan kasar daga Talauci. Rahoton yace, abin damuwar ma shine Gwamnatin Najeriya bata iya biyan mafi karancin Albashin a lokuta da yawa sannan kuma Gwamnatocin jihohi suma basa iya biya saboda karancin kudi. Sannan Rahoton yace wannan mafi karancin Albashin yawanci ma'aikata ba zasu sameshi ba saboda yawanci kamfanoni basu da ma'aikata da yawa inda wasu kuma manoma ne da sauran kananan ma'aikata. Hakan na zuwane a yayin da ake shirin karawa shugaban kasa, da sauran manyan 'yan siyasa...
Lokaci ya ƙure wa Amaechi kan neman takarar shugaban ƙasa – Wike

Lokaci ya ƙure wa Amaechi kan neman takarar shugaban ƙasa – Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya ce lokaci ya ƙure wa tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi kan yunkurinsa na neman takarar shugabancin Najeriya. Wike wanda ya bayyana haka a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels Politics Today, ya ce ƴan Najeriya ba za su zaɓi Amaechi a zaɓen 2027 ba. Amaechi wanda yake cikin haɗakar jam'iyyar ADC waɗanda ke yunkurin kalubalantar shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani na kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a 2022. Amaechi dai ya fice daga jam'iyyar APC zuwa ADC a fafutukar da yake yi na neman kujerar shugaban ƙasa. Sai dai, Wike ya ce Amaechi ba zai samu tikiti a jam'iyyar ADC ba don shiga takara a 2027. "Amaechi da kansa ya sani cewa ba zai samu tikiti ba. Na ji yana ce...
‘Ba mu cire arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar wankin ƙoda ba’>>Inji Gwamnatin Tarayya

‘Ba mu cire arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar wankin ƙoda ba’>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Ma'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta rahotanni da ke cewa babu marasa lafiya daga arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin rage farashin wankin ƙoda da gwamnatin ƙasar ta amince da shi ba. Wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce labarin ba shi da kamshin gaskiya. Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne dai ya amince da rage farashin wankin ƙoda a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar. Karkashin tsarin, za a rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000. Shirin wanda aka ɓullo da shi karkashin shirin Renewed Hope na kyautata rayuwar ƴan Najeriya, yana cikin ƙoƙari da gwamnatin tarayya ke yi wajen rage wa masu fama da cutukan da suka jiɓanci ƙoda raɗaɗi. An fara shirin ne a manyan asibitocin tarayya guda 11 a faɗin ƙasar. As...
Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci – MDD

Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci – MDD

Duk Labarai
Ofishin hukumar kula da jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwa kan ƙaruwar yunwa da talauci da kuma rashin tsaro a Najeriya, inda ta yi kiyasin cewa ƴan ƙasar miliyan 31 na fama da matsalar ƙarancin abinci. Hukumar ta ce akwai sama da yara miliyan goma ƴan ƙasa da shekara biyar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. Bayanin haka ya fito ne a taron da gwamnatin tarayya da hukumar suka gudanar yayin bikin ranar Jin-Ƙai ta Duniya na 2025, wanda aka gudanar ranar Talata a Abuja, mai taken "ƙarfafa haɗin gwiwa a duniya da kuma tallafawa al'ummomi". Hukumar ta ce ya kamata a ɗauki matakai cikin gaggawa domin rage barazanar ƙaruwar matsalar. Jami'in hukumar ta jin-ƙai a Najeriya, Mohamed Fall, ya bayyana cewa bikin ranar ta bana ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ra...
Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima

Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima

Duk Labarai
Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 - Buba Galadima. Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NNPP kuma na kusa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai yi matuƙar wuya Kwankwaso ya haɗa kai da jam’iyyar domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027. Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels , inda ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna adawa ga Kwankwaso ta hanyar goyon bayan Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, duk da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsige shi. Ya ce Kwankwaso ba ya buƙatar dogaro da APC a siyasa, yana mai tunatar da cewa ya kayar da jam’iyyar a Kano a baya. “Kwankwaso bai taɓa gaya min cewa zai mara wa Tinubu baya a 2027 ba,” in ji shi. Galadima ya ƙar...