Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Zuwa yanzu, Shugaba Tinubu ya shafe kwanaki 181 a kasashen waje tun bayan hawansa mulki

Zuwa yanzu, Shugaba Tinubu ya shafe kwanaki 181 a kasashen waje tun bayan hawansa mulki

Duk Labarai
Jam'iyyar ADC ta caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen waje. Jam'iyyar ta bayyana hakane ta bakin kakakinta, Bola Abdullahi inda yace ana kashe kudaden Talakawa wajan tafiye-tafiyen shugaban kasar. Ya bayyana cewa, wannan shine karo 40 da shugaba Tinubu zai bar Najeriya tun bayan hawansa mulki kuma ya kwashe kwanaki 181 a kasashen waje. Sanarwar tace wannan kusan watanni 6 kenan da shugaba Tinubu ya kwashe a kasashen wajan. ADC tace tana Allah wadai da irin wadannan tafiye-tafiyen na shugaban kasa musamman ganin cewa babu wani abin ci gaba da hakan ya kawowa kasarnan.
Kalli Bidiyon wasu mata zuciyarsu kamar zata fashe saboda jin Haushi da hassadar auren Rahama Sadau

Kalli Bidiyon wasu mata zuciyarsu kamar zata fashe saboda jin Haushi da hassadar auren Rahama Sadau

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Murja Kunya ya bayyana cewa wasu mata na nan zuciya kamar zata fashe da haushi da hassada saboda auren Rahama Sadau. Ta baiwa Rahama Sadau shawarar ylta ci gaba da boye mijinta dan kada wasu su ganshi su yi yunkurin rabata dashi. https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7537856619950951686?_t=ZS-8ysgQ9lDJzN&_r=1 https://vt.tiktok.com/ZSSKjraSP
Duk ofis din Abuja na shigesu in banda ‘yan kadan, kuma ba kirana ake ba, ni ke zuwa neman na kaina>>Mansurah Isah

Duk ofis din Abuja na shigesu in banda ‘yan kadan, kuma ba kirana ake ba, ni ke zuwa neman na kaina>>Mansurah Isah

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana cewa kusan duk ofis din dake Abuja ta shigesu in banda kadan. Tace ba kiran ta ake ba, ita ke zuwa neman na kanta. Mansurah Isah ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita inda tace Dangote bai daina neman kudi ba dan haka itama ba zata zauna ba. https://www.tiktok.com/@nassxee_hausa_tv/video/7536909875201182982?_t=ZS-8yseQa5t6xM&_r=1
Shugaban Jami’ar Tarayya Dake Lafia Kenan, AbdulRahman Yake Sanya Hannu A Jikin Rigunan Daliban Da Suka Kammala Karatu A Jami’ar, Inda Ya Hore Su Da Su Kasance Masu Da’a A Yayin Bukukuwan Kammala Karatun

Shugaban Jami'ar Tarayya Dake Lafia Kenan, AbdulRahman Yake Sanya Hannu A Jikin Rigunan Daliban Da Suka Kammala Karatu A Jami'ar, Inda Ya Hore Su Da Su Kasance Masu Da'a A Yayin Bukukuwan Kammala Karatun Tun a farko dai hukumar gudanarwar jami'ar tarayya ta garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa, ta soke duk wani biki da sunan murnar kammala karatu sakamakon wani mummunan hadarin da ya auku na wani babur mai kafa uku a yayin murnar kammala karatun da ake yi a cikin makarantar.
Ji Yadda Ta Kaya Tsakanina Da Shugaban Hukumar EFCC A Yayin Bada Belina -Aminu Tambuwal

Ji Yadda Ta Kaya Tsakanina Da Shugaban Hukumar EFCC A Yayin Bada Belina -Aminu Tambuwal

Duk Labarai
Yadda Ta Kaya Tsakanina Da Shugaban Hukumar EFCC A Yayin Bada Belina -Aminu Tambuwal. "A Lokacin Da Lauyoyina Suka Je Wajen Shugaban EFCC Domin Neman A Bada Ni Beli, Ya Ce Sai Na Kawo Wadanda Za Su Taaya Min. Na Ce Su Koma Su Gaya Masa Na Taɓa Zama Kakakin Majalisa, Na Yi Wa’adin Gwamna Har Sau Biyu, Kuma Yanzu Ina Majalisar Dattawa. Don Haka Ina Iya Tsayawa Kaina Domin Belin Kaina", Cewar Aminu Waziri Tambuwal Daga Jamilu Sani RarahSokoto
Shi dai Wandabya sai min GLK dinnan ya kuma bude min babban Shago, ina zaune a Otal yace in tashi daga Otal in nemo gida kalar wanda nake so ya saimin>>Rahama Saidu

Shi dai Wandabya sai min GLK dinnan ya kuma bude min babban Shago, ina zaune a Otal yace in tashi daga Otal in nemo gida kalar wanda nake so ya saimin>>Rahama Saidu

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta bayyana cewa, shi dai wanda tace bata taba haduwa dashi ba ya sai mata Motar GLK da bude mata babban shago, haka yace ta tashi daga Otal ta nemo gida kalar wanda take so ya siya mata. Rahama tace bata jin dadin irin yanda ake cewa wai kanta ta bayar aka bata morlta. https://www.tiktok.com/@juicylifestyle7/video/7538206815054597382?_t=ZS-8yscCkazHbl&_r=1
Kalli Bidiyo: Da Sheikh Salihu Zaria zai daina Tiktok da matsalar Tiktok ta zo karshe saboda duk wata fitsararriya da muryarsa take amfani>>Inji Baffa Hotoro

Kalli Bidiyo: Da Sheikh Salihu Zaria zai daina Tiktok da matsalar Tiktok ta zo karshe saboda duk wata fitsararriya da muryarsa take amfani>>Inji Baffa Hotoro

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Baffa Hotoro yace yawanci 'yan mata da basu jin magana da kuma karuwai da muryar Sheikh Salihu Zaria suke amfani a Tiktok. Malamin yace da Sheikh Salihu Zaria zai daina wa'azi da matsalar Tiktok ta kau. Yace kuma irin su Sheikh Salihu Zaria ne wai ke kare Izalar Jos. Kalli Bidiyonsa a kasa: https://www.tiktok.com/@jrbunza/video/7537643442587864325?_t=ZS-8ysb98Oa6r2&_r=1
Ko dai a biya mana bukatunmu nan da kwanaki 7 ko mu tsunduma yajin aiki>>Inji Kungiyar Kwadago

Ko dai a biya mana bukatunmu nan da kwanaki 7 ko mu tsunduma yajin aiki>>Inji Kungiyar Kwadago

Duk Labarai
Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gaggauta biya mata bukatunta nan da kwanaki 7 ko kuma ta tsunduma yajin aiki. Kungiyar ta bukaci gyaran Fansho ne da kuma zargin karkatar da wasu kudaden ma'aikata. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da shugaban kungiyar Joe Ajaero ya sakawa hannu. Yace idan gwamnati bata biya musu bukata ba nan da kwanaki 7 akwai yiyuwar su shiga yajin aiki