Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Allah ya tsynewa me karya, Sheikh Salihu Zaria ya gayawa Ministan tsaro, Muhammad Badaru kan ikirarin da ministan yayi cewa an sami tsaro a Arewa

Kalli Bidiyo: Allah ya tsynewa me karya, Sheikh Salihu Zaria ya gayawa Ministan tsaro, Muhammad Badaru kan ikirarin da ministan yayi cewa an sami tsaro a Arewa

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya bayyana cewa, Allah ya tsinewa me karya kuma wanda bai ce amin ba Allah ya hada dashi. Ya bayyana hakane a wani wa'azinsa da ya watsu sosai. Malam ya soki Ministan sosai inda yace ba gaskiya bane abinda ministan ya fadi. https://www.tiktok.com/@ustazbabaa/video/7535964804993912120?_t=ZS-8yjmJor8CLw&_r=1
Gwamnan Kano ya sallami masu taimaka masa guda biyu

Gwamnan Kano ya sallami masu taimaka masa guda biyu

Duk Labarai
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sallamar masu taimaka masa guda biyu bisa laifuffuka daban-daban, sannan aka wanke guda ɗaya bayan kwamitocin bincike sun gabatar da rahoton binciken su. Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Musa Tank Muhammad ya fitar. Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da sallamar Abubakar Umar Sharada, babban mai taimaka wa gwamna kan tattara jama'a bayan kwamitin binciken ya gano shi ne ya kitsa yadda aka yi belin wanda ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Haka kuma gwamnan ya amince da sallamar Tasiu Al'amin Roba bayan kwamitin bincike ya tabbatar da hannunsa a kwana da kayan tallafin a rumbun gwamnati na Sharaɗa, wanda kuma tuni aka gabatar da shi a ...
Da Duminsa: Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi aure, Ji bayani game da wanda ta aura, a ina aka daura

Da Duminsa: Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi aure, Ji bayani game da wanda ta aura, a ina aka daura

Duk Labarai
Rahotanni na bayyana cewa an ɗaura auren jaruma Rahama Sadau a Kaduna a yau Asabar. Wasu makusantan ta sun tabbatar da daura auren a masallacin Masallacin Atiku Auwal Unguwan Rimi, tare da angonta Ibrahim Garba. An ɗaura auren ne kan sadaki Naira 300,000. Abokan sana'arta da suka hada da Ali Nuhu, Hassan Giggs da Maryam Booth duka sun tayata murna.
Idan PDP ta yi nasarar shawo kan tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2027, babu wanda zai iya kayar dashi>>Sule Lamido

Idan PDP ta yi nasarar shawo kan tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2027, babu wanda zai iya kayar dashi>>Sule Lamido

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da zama ɗan takarar jam'iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2027, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da su yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin tsohon shugaban a kan ya koma jam'iyyar ya tsaya takara. "Ina tunanin ya kamata PDP ta janyo shi: shi ne ya fi dacewa ya mata takara. Duk wani ɗantakara da PDP za ta tsayar, ƴan Najeriya za su zaɓe shi," in ji tsohon gwamnan kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da tashar Channels. Lamido ya bayyana Jonathan a matsayin wanda ya fahimci ƙasar kasancewar ya yi mulki a baya, kuma ya san yadda zai yi mu'amalanci mulkin ƙasar. Ya ce ba su da wani ɗantakara daga kudancin Najeriya da ya fi tsohon shugaban ƙasar idan ana b...
Fasto Adeboye ya bayyana ranar da zai koma ga Allah

Fasto Adeboye ya bayyana ranar da zai koma ga Allah

Duk Labarai
Babban Faston Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya sake bayyana hasashe kan yadda zai rabu da duniya. Ya ce zai mutu cikin lumana, a ranar Lahadi, bayan ya halarci cocin kuma ya ci sakwara, abincin da yafi so. Da ya ke jawabi a rana ta huɗu na babban taron cocin na kasa da kasa mai taken “The Overcomers”, Fasto Adeboye ya jaddada cewa mutuwa ba sai da ciwo ba. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Faston ya taba bayyana wannan hasashen shekaru biyu da suka gabata, inda ya ce: “Zan mutu ne a ranar Lahadi, bayan na halarci coci, na ci sakwara da nake so, sannan in rabu da duniya ba tare da wani ciwo ba.” Faston ya ce mutuwarsa za ta kasance ta gaggawa kuma salin-alin zai mutu.
Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyan 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba”>>Inji Gwammati

Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyan 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba”>>Inji Gwammati

Duk Labarai
"Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyqn 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba". Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire takunkumin da aka saka kan asusun Hukumar Shirin Zuba Jarin Jin Kai ta Ƙasa “National Social Investment Programme Agency (NSIPA)”, wanda ya kai ga sakin sama da Naira biliyan 493 domin tallafawa gidaje miliyan biyar a fadin ƙasar. Tun a ranar 8 ga Janairu, 2024 ne aka dakatar da Ministar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr Betta Edu, tare da umartar Hukumar Yaƙi da Laifukan Tattalin Arziki da Kuɗi (EFCC) ta gudanar da bincike kan duk wasu harkokin kuɗi na ma’aikatar da hukumomin da ke karkashinta. Haka kuma, Shugaban Ƙasa ya kafa kwamiti karkashin jagorancin Ministan Kudi, Wale Edun, domin duba tsarin kuɗi na shirin jin kai da inganta shi do...