
Rahotanni na bayyana cewa an ɗaura auren jaruma Rahama Sadau a Kaduna a yau Asabar.
Wasu makusantan ta sun tabbatar da daura auren a masallacin Masallacin Atiku Auwal Unguwan Rimi, tare da angonta Ibrahim Garba.
An ɗaura auren ne kan sadaki Naira 300,000.
Abokan sana’arta da suka hada da Ali Nuhu, Hassan Giggs da Maryam Booth duka sun tayata murna.


