Tinubu ba ya jin shawarar ƴan Najeriya – Babachir
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal ya ce babban dalilin da ya sa ya bi haɗakar ƴan hamayya a ƙasar shi ne "rashin jin shawarwarin" da shi da kuma sauran ƴan Najeriya ke bai wa shugaban ƙasar Bola Tinubu.
Babachir na cikin ƴan siyasar Najeriya masu hamayya da suka fi jan hankali bayan ganin su cikin waɗanda suka ja tunga suka dunƙule domin samar da jam'iyyar da za ta ƙalubalanci shugaba Tinubu a zaɓen shekara ta 2027.
Ƴan adawar sun zargi gwamnatin Tinubu da gazaw...








