Sunday, December 14
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hadimin Buhari Shugaban PCNGi

Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hadimin Buhari Shugaban PCNGi

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ismael Ahmed, tsohon hadimin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayin Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi). Wannan shiri na gwamnati na da nufin rage radadin cire tallafin fetur ta hanyar samar da makamashi mai araha da tsafta. Ismael Ahmed ya kasance mai ba Buhari shawara kan Shirin Tallafin Jama'a tsakanin 2018 zuwa 2022. Ya kammala karatunsa na lauya a Jami’ar Abuja, sannan ya samu digirin digirgir a fannin Hulɗar Ƙasashen Duniya daga Jami’ar Webster da ke Amurka.
Da Duminsa: Kasar Faransa ta haramta shan taba a bainar jama’a

Da Duminsa: Kasar Faransa ta haramta shan taba a bainar jama’a

Duk Labarai
Kasar Faransa ta Haramta shan taba sigari a bainar jama'a. Kasar tace ta haramta shan taba a wajan shakatawa dake gabar tekuna da wajan jiran ababen hawa da sauransu. Tun a baya dai kasar take ta bayyana aniyar son hana shan taba amma sai wannan karin ta samu nasarar aiwatar da aniyarta. Rahotanni na bayabayannan sun ce akalla mutane miliyan 7 ne ke mutuwa saboda taba sigari a Duniya.
Talakawa na karuwa sosai a Najeriya, mutane da yawa basa samun Naira dubu biyar a rana>>Inji Bankin Duniya

Talakawa na karuwa sosai a Najeriya, mutane da yawa basa samun Naira dubu biyar a rana>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Bankin Duniya ya bayyana cewa, Talakawa na karuwa sosai a Najeriya dama wasu sauran kasashe 38 na Duniya. Bankin yace hakane a wani babban rahoto da ya fitar tun bayan bullar cutar Korona a shekarar 2020. Bankin yace jimullar mutane Miliyan 421 ne ke fama da matsanancin talauci a Duniya. Bankin ya kara da cewa, mutanen basa samun akalla Dala $3 a kullun wanda kwatankwacin Naira dubu biyar kenan. Bankin ya alakanta hakan da matsalolin tsaro da sauransu. Ya kuma yi gargadin yawan matalautan na iya karuwa zuwa mutane Miliyan 435 nan da shekarar 2030.
Likita ya gargadi masu amfani da man kara hasken fata inda ya bayyana munana cutukan da zasu iya kamasu

Likita ya gargadi masu amfani da man kara hasken fata inda ya bayyana munana cutukan da zasu iya kamasu

Duk Labarai
Kungiyar likitoci ta gargadi masu shafa ma kara hasken fata da cewa suna cikin hadarin kamuwa da munanan cutuka irin su ciwom suga, Kansa, da ciwon Koda. Dan haka kungiyar Likitocin me suna NAD ta bayyana cewa zai fi kyau mutane su rika barin fatarsu yanda take dan hakan zai fi basu kwanciyar hankali. Shugaban Kungiyar Likitocin, Prof. Dasetima Altraide ne ya bayyana hakan a wajan wani taron karawa juna Sani da ya faru a Legas. Yace yawanci sinadaran da aka hada man dasu ne ke jefa mutanen dake amfani da mayukan hasken fatar cikin matsalar rashin lafiya.
Allah Sarki:Ji bayani dalla-dalla yanda aka tursasa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC ba dan yana so ba, ashe har jami’an tsaro aka tura masa dan tsoratashi

Allah Sarki:Ji bayani dalla-dalla yanda aka tursasa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC ba dan yana so ba, ashe har jami’an tsaro aka tura masa dan tsoratashi

Duk Labarai
Rahotanni sun ce tursasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje aka yi ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC ba dan yana so ba. Daily Trust ta ruwaito cewa daya daga cikin shuwagabannin tsaron Najeriya ne ya je har gida ya bukaci Ganduje da ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC. Wani na kusa da Ganduje yace sun kadu sosai da abinda ya faru. Saidai a takardar ajiye aiki da Ganduje ya aikewa jam'iyyar APC, yace ya sauka ne dan mayar da hankali wajan kula da lafiyarsa. Rahoton yace wani gwamna daga Arewa maso gabas da wani daga Arewa sun je yiwa Ganduje jaje. Ana rade-radin cewa, An cire Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC ne dan kokarin kawo 'yan siyasa irin su Dr. Rabiu Musa Kwankwaso cikin jam'iyyar.
Da Duminsa: “Akwai yiyuwar Kwankwaso ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC”

Da Duminsa: “Akwai yiyuwar Kwankwaso ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC”

Duk Labarai
Wani jigo a jam'iyyar APC da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa, akwai alamu masu karfi dake nuna cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar. A hirarsa da jaridar Guardian ya bayyana cewa, bayan komawar Kwankwaso APC akwai kuma yiyuwar zai zama shugaban jam'iyyar. Hakan na zuwane kwana daya bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukamin shugaban jam'iyyar APC. Dan APC din ya bayyana cewa, matsawa Ganduje akayi ya sauka daga kan kujerar tasa ba dan yana so ba. Da aka tambayeshi ko saukar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC zai iya sa Tinubu ya rasa kuri'ar Kano, sai yace hakan ba lallai ya faru ba domin duk da sauke Ganduje daga mukaminsa har yanzu yanawa uwar jam'iyyar APC biyayya.
Ina da Burin samun kudin shiga Naira Biliyan 30 kullun>>Dangote

Ina da Burin samun kudin shiga Naira Biliyan 30 kullun>>Dangote

Duk Labarai
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana xewa kamfaninsa na yin takin zamani suna tsammanin zai rika samar da kudin shiga da suka kai dala Miliyan $20 kullun. Yace kuma suna tsammanin kamfanin zai samar da kudaden shigar da suka kai dala Biliyan $70. Ya bayyana hakane yayin ziyarar da shuwagabannin hukumar hadahadar kasuwancin hannun jari suka kai masa matatar man sa dake Legas. Sun bashi tabbacin taimakawa dan saka kamfanin nasa na yin takin zamani a kasuwar saye da sayarwar hannun jari.
An nada magajin Ganduje

An nada magajin Ganduje

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa an nada mataimakin shugaban APC na yankin Arewa, Ali Bukar Dalori dan ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riko. Hakan na zuwane yayin da aka kira taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar da zai tattauna dan nemo mafita bayan Saukar Ganduje. Ganduje ya mika takardar barin aiki inda yace yayi hakan ne saboda ya samu damar kula da lafiyarsa.