Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai mayar da Gwamna Fubara kan mukaminsa na Gwamnan jihar Rivers, ji sharudan ban mamaki da aka gindaya masa

Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai mayar da Gwamna Fubara kan mukaminsa na Gwamnan jihar Rivers, ji sharudan ban mamaki da aka gindaya masa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da Gwamna Simi Fubara na jihar Rivers kan mukaminsa na gwamnan jihar. Saidai an gindayawa gwamnan Sharuda kamar haka: Ba zai sake tsayawa takarar gwamnan ba a zaben shekarar 2027. Zai yadda Wike ya tsayar da 'yan takarar shuwagabannin kananan hukumomi 23 dake fadin jihar. Hakanan ya yadda ya biya 'yan majalisar jihar dakewa Wike Biyanna su 27 hakkokinsu da ya dakatar, idan ya yadda da hakan, 'yan majalisar ba zasu yi yunkurin tsigeshi ba.
Kalli yanda Wata mamakon Gobara da ba’a san daga inda ta taso ba ta barke a kasar Israyla tana ta yaduwa sosai

Kalli yanda Wata mamakon Gobara da ba’a san daga inda ta taso ba ta barke a kasar Israyla tana ta yaduwa sosai

Duk Labarai
Wata mamakon gobara ta barkena tsakiyar kasar Israyla inda take ta yaduwa sosai. Gobarar da ba'a san inda ta samo Asali ba ta tashine a birnin Ness Ziona kuma 'yan kwana-kwana na ta kokarin kasheta. Rahotanni sun ce an tattaro ma'aikatan kwana-kwana daga yankuna daban-daban dan su taimaka a kashe gobarar. Hukumomi sun ce Tuni aka fara kwashe mutane daga gidajen da Gobarar ta durfafa.
Kalli Yadda Aka Yafawa Ka’aba Sabuwar Riga Albarkacin Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1447 Bayan Hijira

Kalli Yadda Aka Yafawa Ka’aba Sabuwar Riga Albarkacin Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1447 Bayan Hijira

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Yadda Aka Yafawa Ka’aba Sabuwar Riga Albarkacin Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1447 Bayan Hijira.
Dattijon Arziki, Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekara 101 A Duniya

Dattijon Arziki, Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekara 101 A Duniya

Duk Labarai
Dattijon Arziki, Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekara 101 A Duniya. ….Yana da ’ya’ya kimanin 100 da jikoki 406, da tattaba-kunne 100, wadanda su ma suka gaje shi a fannin haddar Kur’ani Daga Ishaq Ismail Musa An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar 2 ga watan Muharram a shekara ta 1346 bayan hijira, inda a gobe Juma’a, 2 ga Muharram na shekarar 1447, yake cika shekaru 101 cif a ban kasa. Duk da cewa iyalai da almajiran Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi ba su yi wani biki don taya shi murnar cika shekara 100 a duniya, amma masoya da almajiran Shehin Malamin sun bayyana farin cikinsu da yi masa addu’o’i musamman a dandali daban-daban na shafukan Intanet. Sun yaba da irin hidimar da ya yi wa Musulunci da Bil Adama, inda suka jinjina rawar da ya taka a matsayinsa na s...
Malaman Kwalejin Kimiyya da fasaha na jihar Kaduna sun koka da cewa, Matasa masu bautar kasa sun fi su Albashi me kyau

Malaman Kwalejin Kimiyya da fasaha na jihar Kaduna sun koka da cewa, Matasa masu bautar kasa sun fi su Albashi me kyau

Duk Labarai
Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kaduna watau Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria sun koka da karancin Albashi inda suka ce matasa masu bautar kasa sun fi su daukar albashi me kyau. Hakanan malaman Kwalejin ilimi ta jihar, College of Education, Gidan Waya suma sun koka akan irin wannan lamari. Jaridar Punchng ta ruwaito cewa, malaman Makarantar na daukar albashin 63,000 zuwa 65,000. A yayin da su kuma matasa masu bautar kasa ake biyansu Naira 77,000 duk wata. Malam sun ce wannan cin fuska ne kuma ta yaya mutum mai iyali zai iya gudanar da rayuwarsa da Albashin Naira 65,000 a wata? Rahoton yace malaman zun zargi cewa hakan nuna halin ko in kula ne a bangaren ili a jihar, wasu daga cikin malaman dai na da kwarewa ta shekaru 10. Rahoton yace wannan dalili yasa malamai su...
Fada ya kare tsakanin mu, mun shirya>>Wike da Fubara bayan da Shugaba Tinubu ya sasantasu

Fada ya kare tsakanin mu, mun shirya>>Wike da Fubara bayan da Shugaba Tinubu ya sasantasu

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa a yanzu babu sauran rashin jituwa tsakanisa da dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Ya bayyana hakane bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da daren ranar Alhamis. Wike yace komai ya wuce. Shima Fubara ya bayyana cewa zaman lafiya ya dawo jihar Rivers inda ya bayyana jin dadinsa da ganin wannan rana da suka yi sulhu shi da Wike.
Duk wanda ke samun kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin a wata talaka ne dan haka ba za’a karbi Haraji a hannunsa ba>>Inji Gwammatin Tinubu

Duk wanda ke samun kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin a wata talaka ne dan haka ba za’a karbi Haraji a hannunsa ba>>Inji Gwammatin Tinubu

Duk Labarai
A jiyane shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar canja fasalin Haraji hannu. Daya daga cikin abinda dokar ta kunsa shine cewa ba za'a karbi Haraji a hannun wadanda ke samun kasa da naira 250,000 a wata ba saboda talakawa ne. Shugaban kwamitin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kafa dan kula da canja fasalin dokar harajin, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan. Ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV bayan da shugaba Tinubu ya sakawa dokar hannu. Yace a yanzu masu daukar 250,000 a wata ko kasa da haka an sakasu a cikin jerin Talakawa.