Ji bayani dalla-dalla: Shugaba Tinubu ne yacewa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC
Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa bayan kwashe ƙasa da shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan.
"Da gaske ne Ganduje ya sauka tun jiya (Alhamis) aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a yau da safe (juma'a) ya miƙa takardar," in ji majiyar.
Hakan na zuwa ne bayan wani rudani da aka samu kimanin mako ɗaya da ya gabata a lokacin taron jam'iyyar ta APC na arewa maso gabashin ƙasar.
A lokacin taron, wasu daga cikin ƴan jam'iyyar sun nuna fushi kan rashin bayyana sunan mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima a matsayin wanda zai mara wa Tinubu baya takarar shugab...







