Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Israyla ta kaiwa tashar Nùkiliya din kasar Ìràn mafi tsaro hari

Israyla ta kaiwa tashar Nùkiliya din kasar Ìràn mafi tsaro hari

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni daga kasar Iran na cewa, jiragen yakin kasar Israyla na ci gaba da ludugen wuta a kasar. Rahotanni sun ce yanzu haka jiragen sun yiwa tashar Nùkiliya mafi tsaro a kasar Iran me suna FORDO luguden bamabamai inda rahotanni suka ce an ji karar fashewar abubuwa har sau biyu. Ita dai wannan tashar Nokiliya a karkashin kasa take kuma an ginata ne da cewa bam din Buñkèr Bustèr ba zai iya lalata ba watau bam me tono kasa. Rahotanni sin ce taba wannan gurin zai iya harzuka ka...
Allah Sarki: ‘Yan Tàwàyèn Hòùthì daga kasar Yèmèn sun zama na farko a Duniya da suka goyi bayan Ìràn ba da baki ba, yanzu haka sun cillawa Israyla makami kuma Israylan ta kasa tareshi

Allah Sarki: ‘Yan Tàwàyèn Hòùthì daga kasar Yèmèn sun zama na farko a Duniya da suka goyi bayan Ìràn ba da baki ba, yanzu haka sun cillawa Israyla makami kuma Israylan ta kasa tareshi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni daga kasar Israyla na cewa, 'yan Tawanyen Houthì na kasar Yemen sun jefa mata makami me linzami. Duk da yake cewa, sojojin kasar, IDF sun ce zasu tare amma sun kasa tareshi, sai da ya sauka. Zuwa yanzu dai ba'a tabbatar da irin barnar da makamin yayi ba. Hoùthì dai na daga cikin masu goyon bayan kasar Ìran a ko da yaushe
Sai da na gayawa Shugaban Amurka cewa zamu kaiwa Ìràn hari kuma ya amince min>>Benjamin Netanyahu ya karyata kasar Amurka kan ikirarin cewa bata da hannu a kaiwa Ìràn hari

Sai da na gayawa Shugaban Amurka cewa zamu kaiwa Ìràn hari kuma ya amince min>>Benjamin Netanyahu ya karyata kasar Amurka kan ikirarin cewa bata da hannu a kaiwa Ìràn hari

Duk Labarai
Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sai da ya sanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump kamin ya kaiwa Iran hari. Yace kuma Trump ya amince. Yace amma ba zai ari bakin Trump ya ci mai albasa ba, zai faa da bakinsa. A baya dai, Sakataren harkokin wajen Amurkar, Marco Rubio ya bayhana cewa, basu da hannu a kaiwa kasar Ìràn hari.
Kasar Ìran tace ta fice daga tattaunawar sulhun mallakar makamin kare dàngì

Kasar Ìran tace ta fice daga tattaunawar sulhun mallakar makamin kare dàngì

Duk Labarai
Kasar Iran ta sanar da ficewa daga tattaunawar sulhu kan mallakar makamin kare danginta. Kafafen yada labarai na kasar Iran din sun tabbatar da hakan inda hakan ke zuwa yayin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ke gargadin Iran din da ta yadda a ci gaba da tattaunawa ko hare-haren da za'a kai mata nan gaba yafi na yanzu muni. A ranar Lahadi me zuwane dai ake tsammanin cewa za'a ci gaba da tattaunawar Sulhun amma yanzu Iran tace ta fice daga tattaunawar. Hakan na iya kara kazanta fadan inda kasar Amurka na iya shigowa cikin fadan.
Tsohon Tsageran Naija Delta, Tampolo yawa shugaban kasa, Tinubu alkawarin kuri’u Miliyan 10 a zaben 2027

Tsohon Tsageran Naija Delta, Tampolo yawa shugaban kasa, Tinubu alkawarin kuri’u Miliyan 10 a zaben 2027

Duk Labarai
Wata kungiya karkashin tsohon tsageran Naija Delta, Tampolo ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin kuri'u dubu 10 a zaben 2027. Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar me suna Comrade Sunday Adekanbi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar 'yancin Najeriya a Abuja inda ya jawo hankalin 'yan Najeriya da su shiga kungiyar. Yace a shekaru 2 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi yana Mulki, ya dora Najeriya a Turbar ci gaban tattalin arziki. Yace zasu yi aiki bisa jagorancin Tampolo dan tattaro kan 'yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027.
Masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Ìràn mallakar makamin kare dangi ba saida taimakon Amurka

Masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Ìràn mallakar makamin kare dangi ba saida taimakon Amurka

Duk Labarai
Wani Rahoto daga kafar Newsweek yace masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Iran mallakar makamin kare dangi ba. Rahoton yace dole sai kasar Amurkar ta taimakawa Israyla. Rahoton yace ko da ma Amurkar ta taimakawa Israylan, idan dai ba kawar da gwamnati me ci suka yi daga kan mulki ba, za'a dakatar da shirin ne na dan wani lokaci amma za'a ci gaba. Dan haka rahotan yace ko da basu yi nasarar kawar da Gwamnatin kasar daga kan mulki ba, su gurguntata ta yanda mutanen kasar zasu tashi tsaye su nemi sauyin gwamnatin Dimokradiyya. Hakan na zuwane yayin da ake rade-radin kasar Amurka na shirin shiga fadan.
Yanzu-Yanzu: Kàsàr Amùrkà tà shìgà fàdàn Israyla da Ìràn tà aìkà dà manyan jiragen ruwa dauke da jiragen yaki gabas ta tsakiya

Yanzu-Yanzu: Kàsàr Amùrkà tà shìgà fàdàn Israyla da Ìràn tà aìkà dà manyan jiragen ruwa dauke da jiragen yaki gabas ta tsakiya

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, kasar ta aike da jiragen ruwa dauke da jiragen yaki zuwa gabas ta tsakiya. A baya dai Amurka ta nuna goyon bayan ta ga kasar Israyla a harin da ta afkawa kasar Ìràn. Kasar Israyla ta kashe manyan sojoji da masana Kimiyyar Nòkìlìyà na kasar Iran da dama. Zuwa yanzu bai babu wani rahoton babbar martani da Iran ta dauka akan kasar Israyla.
Da Duminsa: Zàngà-zàngà ta barke a kasar Ìràn inda ‘yan kasar ke neman ta mayarwa da Israyla martani me zafi kan kìsàn da tawa manyan mutanen kasar

Da Duminsa: Zàngà-zàngà ta barke a kasar Ìràn inda ‘yan kasar ke neman ta mayarwa da Israyla martani me zafi kan kìsàn da tawa manyan mutanen kasar

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, Zanga-zanga ta barke inda mutanen kasar ke neman kasar tasu ta mayar da martani me zafi kan kasar Israyla. Bidiyo sun bayyana inda aka nuna Iraniyawa maza da mata na kuka suna dauke da hotunan mutanen da aka kashe a kasar. Masana kimiyyar Nòkìlìyà da manyan sojojin kasar da yawa ne aka kashe. Lamarin ya zo da ba zata inda kasar iran din bata tabuka wani kokari na kare harin da aka afka mata ba.
Kafar Yada labaran Amurka me suna Axios ta ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump karya yake da yace bai goyi bayan kaiwa Ìràn hari ba, Zambatar Ìràn din yayi dan kada wadanda suke son kàshèwà su boye

Kafar Axios ta kasar Amurka tace ta gano cewa shugaban kasat Amurka, Donald Trump karya yake da yace baya goyon bayan harin da aka kaiwa kasar Ìràn. Kafar tace ta yi magana da wata majiya 2 daga Israyla wadda ta tabbatar mata da cewa sai da kasar Amurkar ta amince sannan suka kaiwa kasar Ìràn hari. Kafar tace shugaban Amurka Donald Trump ya nuna cewa bai san da harin bane dan yaudarar wadanda suke son kashewa su tsaya kada su boye kamin a kashèsu. Shugaba Trump dai yayi ikirarin cewa, ya gargadi kasar Israyla kada ta kaiwa kasar Iràn hari, amma idan wannan rahoton na kafar Axios ya tabbata, to lallai ya munafurci mutane.