Kudin da ake warewa bangaren lafiya sun yi kadan matuka, ba zasu iya magance matsalar rashin lafiyar da ake fama da ita ba a Najeriya>>Inji Me kudin Duniya, Bill Gates
Me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa kudin da ake warewa bangaren lafiya a Najeriya sun yi kadan.
Yace sam kasafin kuin da ake warewa Najeriya ba zai iya magance matsalar rashin lafiyar da ake fama da ita ba a kasar.
Yace kasafin kudin Najeriya zai fuskanci tangarda musaman shekara me zuwa saboda babu kudin tallafin da aka saba bayarwa.
Bill Gates ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yayin ganawar da yayi dasu a Legas.
Ya ce, Karancin kudin da bangaren kula da lafiyar Najeriya ke fama dashi shine yasa kasar ke kan gaba wajan yawan mutuwar mata masu ciki da jarirai sabuwar haihuwa a Duniya.
Ya kara da cewa mafi yawancin haihuwar da ake yi musamman a Arewacin Najeriya, yawanci a gida ake haihuwa kuma ko da sauran da ake kaiwa Asibiti, akwai asibitocin da basa iya yiw...








