Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bidiyon matar aure tana lalata da wani ya bayyana inda mata suka fito zanga-zanga

Bidiyon matar aure tana lalata da wani ya bayyana inda mata suka fito zanga-zanga

Duk Labarai
Bidiyon matar aure ya bayyana a kafafen safa zumunta inda aka ganta tana lalata da wani mutum. Matar dai ta fito ne daga jihar Anambra. Lamarin yasa matan yankin da take suka fito zanga-zanga inda suke cewa tana kokarin kwace musu maza. Matar dai da aka yi hira da ita tace taĺauci ne yasa ta ta aikata hakan. Tace kuma cin zarafin da mijinta yake mata ya taimaka sosai wajan halin data samu kanta.
Matashiyar ƴar gwaggwarmaya Hamdiyya Shareef ta koma gidansu bayan zargin sace a Sakkwato

Matashiyar ƴar gwaggwarmaya Hamdiyya Shareef ta koma gidansu bayan zargin sace a Sakkwato

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan Najeriya ta samu nasarar hada matashiyar ƴar gwagwarmayan nan, Hamdiyya Shareef da mahaifan ta a Sakkwato bayan batan da ta yi a ranar Laraba. Hamdiyya, wadda ta shahara wajen fafutukar ilimin ‘yan mata da kare hakkin matasa, ta bace a wani hali da ba a san ainihin dalilinsa ba, lamarin da ya tayar da hankulan mahaifan ta da dangin ta da masu goyon bayanta. A cewar Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Sokoto, hadin gwiwa da hanzarin tattara bayanan sirri ne suka taimaka wajen gano inda take cikin koshin lafiya. Kakakin rundunar ya yaba wa ‘yan kasa bisa hadin kan da suka bayar tare da jaddada kudirin rundunar na kare duk wani dan Najeriya, musamman matasa masu rauni. ‘Yan uwanta, cike da hawaye da farin ciki, sun bayyana godiya ga ‘yan sanda da duk wanda ya tsaya musu a ...
Ku Daina Wahalar da kanku an rubuta sakamakon zaben shekarar 2027>>Sowore ya gayawa ‘yan Najeriya

Ku Daina Wahalar da kanku an rubuta sakamakon zaben shekarar 2027>>Sowore ya gayawa ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore kuma dan siyasa ya bayyana cewa an riga an rubuta sakamakon zaben shekarar 2027. Ya bayyana hakane a wata hira da kafar Vanguard ta yi dashi. Inda yace abu daya kawai da 'yan Najeriya zasu yi shine su yi zanga-zanga dan samun zabe me kyau amma tsarin zaben da ake dashi bai da kyau Kuma ya bayyana cewa, ba zai hada kai da Peter Obi ba a zaben shekarar 2027 ba.
Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja

Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja

Duk Labarai
Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja. …jama'a mu yada (sharing) wannan sako domin amfanar sauran jama'a 1) Allah Ya yi rantsuwa da su a cikin alQurani. Qur'an 89:2. 2) Sune Ayyamun Ma'alumat da Allah ya umurci ayi ambaton sa a ciki a suratul Hajj Qur'an 22: 28. 3) Aiki a cikin su yafi falala da lada da soyuwa ga Allah akan duk sauran kwanakin shekara. Bukhari no.926. 4) Ana so a yawaita Subhanallah, Walhamdulilllah, wallahu Akbar wa Lailaha illallah da karatun al-Qurani. Bukhari ya ruwaito. 5) Ana so a bayyana ambaton Allah a ciki domin a tunawa wanda yamanta. Abdullahi Ibn Umar da Abu-Hurairah sun kasance suna shiga kasuwa suna kabbara jamaa na kabbara da kabbarar su. Bukhari ya ruwaito . 6) Aikin Hajji yana cikin Ayukka mafi falala a cikin wadann...
DA ƊUMI-ƊUMI: Atiku, Peter Obi, Amaechi, Kashim Ibrahim-Imam da sauran manyan shugabanni sun fara wani babban taron haɗaka yanzu haka a Abuja, domin tsara yadda za su kayar da Tinubu a zaɓen 2027

DA ƊUMI-ƊUMI: Atiku, Peter Obi, Amaechi, Kashim Ibrahim-Imam da sauran manyan shugabanni sun fara wani babban taron haɗaka yanzu haka a Abuja, domin tsara yadda za su kayar da Tinubu a zaɓen 2027

Duk Labarai
Ana Gudanar Da Taron Haɗaka Tsakanin Manya 'Yan Siyasar Jam'iyyun Hamayya A Nijeriya. A wajen taron an hango Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, shugaban BOT na PDP, Adolphus Wabara, da sauran manyan 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki. An yiwa taron laƙabi da (National Political Consultative Group (North) . Ana sa ran tattaunawa kan makomar siyasar Arewa da haɗa ƙarfi don fuskantar manyan zaɓuka masu zuwa a 2027. Me zaku ce?
Real Madrid ta sanar da ɗaukar Alonso a matsayin sabon kocinta

Real Madrid ta sanar da ɗaukar Alonso a matsayin sabon kocinta

Duk Labarai
Real Madrid ta sanar da ɗaukar Xabi Alonso a matsayin sabon kocinta. Alonso wanda ya buga wa Real ɗin wasa 236 a matsayin ɗan wasanta a baya, ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku. A farkon watan nan ne ya sanar da cewa zai bar Bayer Leverkusen da yake jagoranta. Tsohon ɗan wasan na Liverpool da kuma Sifaniya, ya jagoranci ƙungiyar lashe kofin Bundesliga a bara ba tare da an doke shi ko da wasa ɗaya ba - da kuma German Cup. Alonso wanda yarjejeniyarsa za ta kai har 30 ga watan Yunin 2028, zai maye gurbin Carlo Ancelotti. Ancelotti ya jagoranci wasansa na karshe a Madrid a ranar Asabar, inda a yanzu zai zama sabon kocin ƙasar Brazil. Za a gabatar da Alonso wanda ya lashe Champions League a 2014 lokacin da yake buga wa Madrid kwallo - a gobe Litinin a filin atisayen ƙun...
‘Yadda tsohon mijina ya sake ni bayan ƙwace min kwangilar biliyoyin naira’

‘Yadda tsohon mijina ya sake ni bayan ƙwace min kwangilar biliyoyin naira’

Duk Labarai
Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywood, Masurah Isah ta tabbatar da mutuwar aurenta na biyu, wanda ta bayyana cewa ya zo mata a wani yanayi na ba-zata, kamar almara. Mansurah ta ce ita aure ta yi na soyayya, domin a cewarta, "so makaho nr", amma ashe mijin da wata manufar daban ya zo, ba aure na gaskiya ba. Mansurah ta bayyana haka ne a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, inda BBC ta tattauna da ita tare da tsohuwar jaruma a masana'antar, Fati Mohammad kan zargin matan Kannywood da rashin zaman aure. Da take shimfiɗa, Fati Mohammad ta ce mutane ne suke musu gurguwar fahimta, domin "shi aure ai yana da rai, kuma idan Allah ya kawo ƙarshensa, dole sai ya ƙare. Mutane da yawa aurensu yana mutuwa, amma saboda ba a sansu ba, sai ba za a ji ba," in ji ta. Ta ce yawanci...
Tun ba’a je ko ina ba, Riciki ya kunno kai a jam’iyyar ADC da su Atiku da Peter Obi ke son komawa dan kwace mulki a shekarar 2027

Tun ba’a je ko ina ba, Riciki ya kunno kai a jam’iyyar ADC da su Atiku da Peter Obi ke son komawa dan kwace mulki a shekarar 2027

Duk Labarai
Rahotanni na cewa, riciki ya kunno kai a jam'iyyar ADC da su Atiku da Peter Obi ke son amfani da ita dan tsayawa takarar sugaban kasa a shekarar 2027. Rahotanni sun ce jam'iyyar a asirce ta canja kundin tsarin mulkinta inda ta baiwa sabbi da tsaffin membobinta dama iri daya, ana tunanin ta yi hakanne saboda manyan 'yan siyasa irin su Atiku dake shirin komawa cikinta. Saidai wasu tsaffin 'yan jam'iyyar sun ki amincewa da wannan mataki inda suka ce ba zasu baiwa kowa mukaman sa suke rike dashi ba musamman wadanda suka shiga jam'iyyar daga baya. Saidai wasu 'yan jam'iyyar wanda basu da yawa sun amince da wannan mataki. Ana tunanin 'yan Jam'iyyar Adawa zasu yi amfani da jam'iyyar ADC dan yakar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekara 2027.