Tuesday, July 28
Shadow

Author: Bashir Ahmed

A karin Farko, Najeriya ta fitar da Kwanon Sola(Solar Panel) wanda aka kera a Najeriya zuwa kasar Waje

A karin Farko, Najeriya ta fitar da Kwanon Sola(Solar Panel) wanda aka kera a Najeriya zuwa kasar Waje

Duk Labarai
Najeriya ta kafa Tarihi inda a karin farko ta fitar da Solar Panel, watau Kwanon Sola da ake hada wutar Hasken rana dashi wanda aka hadashia gida Najeriya zuwa kasar Ghana. Wannan ne karin farko da hakan ta faru inda hakan ke nuna irin ci gaban da Najeriya ta samu a wannan fannin. Tuni dai Gwamnati a baya ta dauki matakai dan karfafa wannan bangare.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa mutane 17 da aka samu da manyan Laifuka, ciki hadda Dan majalisa Farouk Lawal, da Janar Mamman Vatsa

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa mutane 17 da aka samu da manyan Laifuka, ciki hadda Dan majalisa Farouk Lawal, da Janar Mamman Vatsa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa wasu masu manyan laifuka su 17 dake tsare a gidajen yarin Najeriya daban-daban. Daga ciki akwai tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Farouk Lawal, da Marigayi janar Mamman Jiya Vatsa, da Herbert Macaulay. Cikin wadanda shugaban ya yafewa badda wanda aka kama da laifin safarar miyagun Kwayoyi. Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka inda yace shugaba Tinubu ya yi wannan yafiyar ne bayan zaman majalisar Iyayen kasa a ranar Alhamis a Abuja. Akwai kuma masu laifi 65 da shugaba Tinubu ya ragewa yawan shekarun da zasu yi a gidan yarin. Akwai kuma masu laifi guda 7 da shugaban ya ragewa hukunci daga hukuncin kisa zuwa Hukuncin daurin rai da rai
Kalli Bidiyon: Nakan Buga Misali da maganganun babban Malami Ibn Taimiyya duk da wasu daga cikin ‘yan Dariqarmu basa son ina hakan>>Inji Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari

Kalli Bidiyon: Nakan Buga Misali da maganganun babban Malami Ibn Taimiyya duk da wasu daga cikin ‘yan Dariqarmu basa son ina hakan>>Inji Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, yana bayar da misali da maganganun Babban Malami, Ibn Taimiyya. Saidai yace wasu daga cikin 'yan darika basa son yana fadin hakan. Malam ya bayyana hakane yayin da yake kira ga kiyaye kalamai akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). https://www.tiktok.com/@hassan.a.hassan.2/video/7557755353786535224?_t=ZS-90PXbyOsLJ3&_r=1
Kalli Bidiyo: Sai yanzu na yadda da masu cewa Sheikh Nura Khalid yana zuwar Wiywiy, inaga kamin yace Sufayene suke fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya dan kurbi Shayin Wiywiy din da ya saba sha>>Inji Malam

Maganar Malam Nura Khalid ta cewa Sufaye ne suka fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta. Daya daga cikin malaman Izala ya mayar masa da raddi inda yace sai yanzu ya yadda cewa Malam Nura Khalid na zuhkar Wiywiy kamar yanda aka fada a baya. Yace kuma yana ga kamin yayi waccan magana ya sha shayin wiwi din da ya saba sha. Yace Malam Nura Khalid Jahili ne sannan abinda yasa ba zai yi wata kakkausar magana akansa ba dan kada dansa ya fito yayi kuka, kamar yanda a baya da aka ce yana shan Wiywiy ya fito ya rika kuka a social media. https://www.tiktok.com/@zaidou1taza/video/7558571476857785611?_t=ZS-90PUuFzQQhU&_r=1
Bama son A gina mana makarantu ko Tituna, A samar mana da tsaro kawai>>Inji Sanata Garba Musa Maidoki daga jihar Kebbi

Bama son A gina mana makarantu ko Tituna, A samar mana da tsaro kawai>>Inji Sanata Garba Musa Maidoki daga jihar Kebbi

Duk Labarai
Sanata Garba Musa Maidoki daga jihar Kebbi ya bayyana cewa, basa bukatar a samar musu da makarantu ko tituna a jiharsu. Sanatan yace matsalar tsaro ta yi kamari a yankinsu ta yanda ya zu abinda kawai suke bukata shine tsaron ba wai a gina musu titi ko Makarantu ba. Ya bayyana hakane yayin zaman majalisar. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1975918730048876615?t=qIRYNyO0HFO_a_SoI9HFxg&s=19
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka hannu dan samar da makarantar horas da ‘yansanda ta musamman da zata dace da zamani

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka hannu dan samar da makarantar horas da ‘yansanda ta musamman da zata dace da zamani

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar bude makarantar horas da 'Yansanda ta musamman hannu. Makarantar me sunan Nigeria Police Training Institutes zata horas da 'yansanda ne game da yanda zasu rika gudanar da ayyukansu daidai da zamani. Masana sun ce wannan sabuwar makarantar ka iya zama ta farko wajan kawo gyara ga ayyukan tsaro a kasarnan
Nima ina goyon bayan a saki Nnamdi Kanu>>Inji Atiku Abubakar

Nima ina goyon bayan a saki Nnamdi Kanu>>Inji Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, yana kira a saki shugaban Kungiyar 'yan Ta'addha ta ÌPÒB dake son kafa kasar Biafra, watau Nnamdi Kanu. Atiku yace ci gaba da rike Nnamdi Kanu kamar budadden ciwo ne ga 'yan Najeriya dake ci gaba da yiwa mutane zafi. Sannan kuma sabawa doka ne. Yace kin bin umarnin kotu data bayar da belinsa kama karyane da kuma take hakki. Atiku yace dan haka yana goyon bayan Zanga-zangar da Sowore ya shirya ta neman a saki Nnamdi Kanu. Yace Najeriya ta gaza idan aka ci gaba da kyale Nnamdi Kanu a tsare
Mun samu ci gaba sosai, Yanzu an daina kiran Najeriya da kasar Cin Hanci da rashawa>>Inji Matar Shugaban kasa, Oluremi Tinubu

Mun samu ci gaba sosai, Yanzu an daina kiran Najeriya da kasar Cin Hanci da rashawa>>Inji Matar Shugaban kasa, Oluremi Tinubu

Duk Labarai
Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta bayyana cewa, an samu ci gaba sosai a mulkin Mijinta, Bola Ahmad Tinubu. Ta bayyana cewa, a yanzu an daina kiran Najeriya da kasar cin hanci da rashawa. Tace idan ta fita zuwa kasashen waje, aka ce daga Najeriya take mutane na son magana da ita. Ta bayyana hakane a yayin ziyarar da ta kai jihar Gombe inda ta kaddamar da wasu ayyukan ci gaba. Ta yi kira ga 'yan Najeriya dasu mayar da hankali wajan yada labarai masu kyau game da kasar.
Yayin da Gwamnatin Tarayya tace Karyace, Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN tace maganar da Amurka ta yi na cewa ana shekye kiristoci da yawa a Najeriya gaskiyane

Yayin da Gwamnatin Tarayya tace Karyace, Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN tace maganar da Amurka ta yi na cewa ana shekye kiristoci da yawa a Najeriya gaskiyane

Duk Labarai
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta goyi bayan kasar Amurka da ta ce ana kashe kiristoci a Najeriya da yawa. Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya bayyana hakan ranar Laraba. Yace kin fadawa kai gaskiya da zargi ba zai kawo karshen matsalar ba Yace karfin hali da fuskantar matsalar tare ne zai kawo yadda da juna a tsakani. Yace tabbas Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya musamman yankunan Arewa na fuskantar Kisa da asarar Dukiyoyi da sauransu. Sanatan kasar Amurka, Ted Cruz ne ya bayyana hakan inda yayi zargin cewa an kashe Kiristoci 52,000 da kona coci-coci 20,000 a Najeriya. Gwamnatin Tarayya dai Tuni ta karyata wannan ikirarin na satan kasar Amurkar.