Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan Najeriya dubu 50 sun yi gudun Hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 2024

‘Yan Najeriya dubu 50 sun yi gudun Hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 2024

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Ingila na cewa 'yan Najeriya 52,000 ne suka yi gudun Hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 2024. Rahoton yace 'yan Najeriya na kan gaba waja yin gudun Hijira zuwa kasar Ingila a tsakanin kasashe wanda ba turawa ba. Hakan na zuwane duk da yake yawan masu yin gudun Hijira zuwa kasar ta Ingila ya ragu da kaso 50 cikin 100. Yawanci 'yan Najeriyar na tafiya ne saboda nema aiki da karatu da sauransu.
Bidiyo Gwanin Ban Tausai:Kalli Yanda ‘Yan Damfara suka yiwa wani Alhaji Wayau suka kwace masa dala $1000 takardun dala $100 suka bashi dala $9 takardun dala daya-daya da sunan sun masa canji

Bidiyo Gwanin Ban Tausai:Kalli Yanda ‘Yan Damfara suka yiwa wani Alhaji Wayau suka kwace masa dala $1000 takardun dala $100 suka bashi dala $9 takardun dala daya-daya da sunan sun masa canji

Duk Labarai
Wasu 'yan Damfara sun yiwa wani Maniyyaci wayau dan jihar Yobe. Sun kwace masa dala $1000 'yan dala $100 inda suka bashi dala $9 watau takardun dala $1. https://www.tiktok.com/@alamin_jiddah2/video/7507337629566766342?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7507337629566766342&source=h5_m&timestamp=1747985554&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7496016997063755575&share_link_id=50ca7b05-abf6-4186-ac66-0b16b714fc5f&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_btm=b5836%2Cb2878&link_reflow_popup_ite...
Kalli Bidiyo: “Shugaban kasa na tashi tsaye ya gaida Kolo”, Inji Wani bayan da shugaba Tinubu ya tashi ya gaishe da Rarara

Kalli Bidiyo: “Shugaban kasa na tashi tsaye ya gaida Kolo”, Inji Wani bayan da shugaba Tinubu ya tashi ya gaishe da Rarara

Duk Labarai
A jiyane aka yi babban taron jam'iyyar APC na kasa a fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankali shine wakar Rarara. https://www.tiktok.com/@dankasuwa149/video/7507291625270562054?_t=ZM-8waVNq4IN53&_r=1 Bayan kammala wakar, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tashi tsaye sun gaisa da Rarara wanda ake ganin hakan babbar girmamawa ce.
Dangote ya kara sa mun tafka mummunar Asara saboda rage farashin man fetur din da yayi jiya>>’Yan kasuwar Man fetur suka koka

Dangote ya kara sa mun tafka mummunar Asara saboda rage farashin man fetur din da yayi jiya>>’Yan kasuwar Man fetur suka koka

Duk Labarai
Kungiyar 'yan kasuwar man fetue ta kasa, IPMAN ta yi martani game da rage farashin man fetur din da matatar man fetur din Dangote ta yi jiya Alhamis. Matatar man fetur din Dangote ta rage Naira 15 akan kowace lita kamar yanda ta sanar a jiya. Saidai shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Chinedu Ukadike yace su lamarin ya zama riba da asara a wajansu, yace yanzu wadanda suka sayi man fetur din a wajan Dangote a tsohon farashi in ba sa'a ba zasu tafka Asara ne. Sannan kuma su 'yan kasuwa dake shigo da man fetur din suma saidai su je su samu man fetur din dake da Arha su siyo. Yace Dangote na amfani da rage farashi ne da ya zama shi ne ke da wuka da nama akan samarwa da raba man fetur a kasarnan.
Ni Madugu ne, nasan hanya, dan haka ku biyoni in kaiku Tudun Min Tsira>>Tinubu

Ni Madugu ne, nasan hanya, dan haka ku biyoni in kaiku Tudun Min Tsira>>Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa shi Madugune wanda ya san hanya dan haka yayi kira ga 'yan Najeriya da su bishi ya kaisu Tudun Mun tsira. Shugaban kasar ya bayyana hakane a waja wani jawabi da yayi ga 'yan jam'iyyar APC a babban taron da jam'iyyar ta gudanar. https://www.youtube.com/watch?v=_il2fpvHoow?si=9rXDxS3JBCuoZnKv Hakanan yace masu kukan za'a mayar da Najeriya jam'iyya daya yace mutane ne suna cikin jirgi suna ganin zai nutse shiyasa suke tserewa.
Gwamnatin tarayya ta hana tankokin dake dakon man fetur tuki da dare

Gwamnatin tarayya ta hana tankokin dake dakon man fetur tuki da dare

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace daga yanzu ba za'a kara barin tankokin dakon man fetur su rika tuki da dare ba. Ta bayyana hakane ta bakin shugaban hukumar kula da hadahadar Man fetur ta kasa, Farouk Ahmed, a wajan wani taro. Yace daga yanzu Direbobin tankar zasu rika tuki ne daga 6 na safe zuwa 6 na yamma. Yace an dauki wannan mataki ne dan magance matsalar hadurran tankar mai wadda ta jawo hasare rayuka da Dukiyoyi q baya. An yi taronne da hadin gwiwar direbobin tanka, da hukumar kiyaye hadurra ta kasa, Road Safety da Kungiyar ma'aikatan fetur na kasa da sauransu. Yace duk direban da aka kama yana tuki da dare zai fuskanci hukunci.
A kasarnan ne fa saboda mugun abu aka kama Mutum da gidaje 750 na sata>>Shugaba Tinubu

A kasarnan ne fa saboda mugun abu aka kama Mutum da gidaje 750 na sata>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana mamaki kan yanda aka kama mutum daya da gidaje guda 750 na sata. Shugaban ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi dashi. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1925602986862026869?t=qws3dWF2gX9hlD6h8_cn_Q&s=19 Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Emefiele ne aka kama da wadannan gidaje wanda tuni an kwace za'a sayar dasu.
Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya

Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya

Duk Labarai
Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya. Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ceto ƴanƙasar da ke maƙale a Saudiyya sakamakon sabbin sauye-sauyen dokokin ayyukan ƙwadogo da hukumomin Saudiyya suka bijiro da su. Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Shehu ne ya gabatar da udurin a yayin zaman majalisar na ranar Laraba. A baya-bayan nan ne dai hukumomin Saudiyya suka bijiro da wasu sauye-sauye kan dokokin da suka shafi ayyukan baƙi a ƙasar, ciki har da daina sabunta takardun izinin aiki a ƙasar ga wasu mutanen. Hon. Muhammad Shehu ya ce sauye-sauyen sun tilasta wa wasu ƴan Najeriya da dame da ke zaune a Saudiyya rasa ayyukansu, yayin da wasu ke fuskantar tsadar kuɗin sabunta takardun...
Ƴansanda sun ceto mai shekara 80 daga hannun masu gàrkùwà a Jigawa

Ƴansanda sun ceto mai shekara 80 daga hannun masu gàrkùwà a Jigawa

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata tsohuwa mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano. Kakakin Rundunar ƴansandan jihar SP Lawan Adam Shiisu Adam ya ce mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta a cikin wani daji na jihar Jigawa mai makwabtaka. ''Bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazuka da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, daga nan ne jami'ansu tare da haɗin gwiwar ƴanbijilanti da na ƙungiyar ƴanbulala suka far wa maharan, bayan ɗauki-b-daɗi kuma suka samu nasarar ceto ta'' SP Shiisu ya ce jami'ansu sun yi nasarar kama wasu manyan ƴanfashin daji biyar da aka jima ana nema ruwa-a-jallo. ''Daga ciki akwai wanda ma har yana tsallakawa jamhuriyar Nijar ya k...