Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan Kasuwar Kwai sun koka da rashin ciniki inda suka nemi Shugaba Tinubu ya kawo musu dauki

‘Yan Kasuwar Kwai sun koka da rashin ciniki inda suka nemi Shugaba Tinubu ya kawo musu dauki

Duk Labarai
Kungiyar masu sana'ar kiwon kaji sun koka da rashin kasuwar kwan kajin inda suka ce hakan ya farune saboda tsadar rayuwa a tsakanin al'umma. Shugaban kungiyar reshen jihar Jigawa, Mr. Hussaini Gumelne ya bayyana hakan yayin da suka kaiwa Gwamnan jihar, Umar Namadi ziyara. Yace sun fara ganin kasuwar Kwan ta yi kasa ne tun bayan da aka cire tallafin man fetur. Inda yace 'yan Najeriya da yawa a yanzu basa iya cin kwai. Ya nemi cewa, Gwamnati ta basu tallafi ta hanyar baiwa membobinsu musamman mata horaswa sannan Gwamnatin ta saka Kwai cikin shirin ta na ciyar da dalibai ta yanda zasu rika samun ana sayen kwan a hannunsu.
Gwamnatin Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da aka sace ga asalin masu su

Gwamnatin Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da aka sace ga asalin masu su

Duk Labarai
Gwamnatin Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da aka sace ga asalin masu su. Gwamnatin Jihar Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da jami’an tsaro suka kwato daga hannun barayin shanu ga asalin masu su cikin wata 15 da suka gabata. Shugaban kwamitin tantance dabbobin da aka kwato, Sheikh Sa’idu Maikwano, ne ya bayyana hakan a wani taro da sakataren gwamnatin jihar Abubakar Nakwada. Taron dai na da nufin tsara sabbin dabaru da hanyoyi masu inganci don tabbatar da nasarar aikin kwamitin, musamman yanzu da jami’an tsaro ke samun nasarori sakamakon karin hare-haren da suke kaiwa a fadin jihar. Dabbobin da aka mayar sun hada da shanu, tumaki da awaki da sauransu. Shugaban kwamitin ya yaba wa Sakataren Gwamnatin jihar, kan yadda yake sa ido yadda ya kamata a kan aikin kwamitin. ...
Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai – Kocin Arsenal

Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai – Kocin Arsenal

Duk Labarai
Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai - Kocin Arsenal. Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ƙungiyar tasa ce ta fi kowacce ƙoƙari a gasar zakarun Turai ta Champions League ta bana duk da kashin da suka sha a hannun Paris St-Germain. BBC Hausa ta rawaito cewa Arsenal ɗin ta je filin wasa na Parc des Princes ne da zimmar rama ƙwallo ɗaya da aka zira mata a gidanta a wasan farko domin kaiwa wasan ƙarshe na gasar. Sai dai duk da damarmakin da suka ƙirƙira, 'yanwasan Arsenal ɗin ba su iya yin nasara ba. Ƙwallayen da Fabian Ruiz da Achraf Hakimi suka ci ne suka taimaka wa PSG din, inda har sai a minti na 76 Bukayo Saka ya farke wa Arsenal ɗaya, inda wasa ya tashi 3-1 gida da waje. "Saura ƙiris, ƙiris ya rage mu sauya sakamakon wasan, amma kuma aka fitar da mu," a cew...
Matasan jam’iyyar APC sun yi zanga-zangar neman a binciki Matawalle a hedikwatar EFCC

Matasan jam’iyyar APC sun yi zanga-zangar neman a binciki Matawalle a hedikwatar EFCC

Duk Labarai
Mambobin kungiyar All Progressives Congress Young Leaders Alliance (APC-YLA) a ranar Juma’a sun gudanar da zanga-zanga a gaban hedikwatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ke Abuja. Sun bukaci hukumar da ta gaggauta dawo da binciken zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Bello Matawalle, wanda yanzu haka shi ne karamin ministan tsaro. Kungiyar, wadda ta bayyana kanta a matsayin wata kungiya mai matsin lamba ta siyasa dake da tushe a Kaduna, ta zargi EFCC da yin shiru game da wannan batu duk da korafe-korafen da dama da kuma alkawarin da ta riga ta dauka na gudanar da bincike a kan tsohon gwamnan jihar Zamfara. A wata takarda da suka mika yayin zanga-zangar, kungiyar ta tambayi dalilin da yasa EFCC ta kasa daukar mataki a kan Matawalle duk da zarge-zargen aikata ba d...
Tuhume-tuhumen EFCC: Yahaya Bello zai san matsayin sa ranar 26 ga watan Yuni

Tuhume-tuhumen EFCC: Yahaya Bello zai san matsayin sa ranar 26 ga watan Yuni

Duk Labarai
Tuhume-tuhumen EFCC: Yahaya Bello zai san matsayin sa ranar 26 ga watan Yuni. Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya Bello daga gwamnatin jihar Kogi ko wata ƙaramar hukuma zuwa asusun makarantar AISA ba, ya kuma karanta wani ɓangare na hukuncin da kotun FCT ta yanke cewa babu umarnin kotu ...
Ku tafi mana Allah raka taki gona>>Gwamnatin Najeriya ta gayawa Kamfanin Facebook da yace zai bar Najeriya saboda an ci shi tara

Ku tafi mana Allah raka taki gona>>Gwamnatin Najeriya ta gayawa Kamfanin Facebook da yace zai bar Najeriya saboda an ci shi tara

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bakin Hukumar kula da yanda ake kasuwanci da baiwa 'yan Najeriya kariya, (FCCPC) tace Kamfaninn Meta me Facebook da Instagram da WhatsApp ko da ya bar Najeriya sai ya biya tarar da aka kakaba masa. An kakabawa kamfanin tarar Dala Miliyan $290 bisa zargin aikata ba daidai ba da bayanan 'yan Najeriya dake amfani da manhajar. Saidai kamfanin yayi barazanar barin Najeriya. Wakilin Hukumar FCCPC, Ondaje Ijagwu, ya bayyana cewa an yiwa kamfanin na META irin wannan tarar a Texas ta kasar Amurka da kasashen Turai da India, South Korea, France da Australia amma duk bai yi barazanar barin wadancan kasashe ba sai Najeriya. Yace kamfanin ya fadi waccan maganane kawai dan ya jawo hankalin mutane amma ya sani ko ya bar Najeriya sai ya biya tarar da ake binsa.
Yawan danyen man fetur din da Najeriya ke fitarwa ya ragu da kaso 4.37 cikin 100

Yawan danyen man fetur din da Najeriya ke fitarwa ya ragu da kaso 4.37 cikin 100

Duk Labarai
Kungiyar kasashe masu arzikin Man Fetur, OPEC ta bayyana cewa, yawan danyen man fetur din da Najeriya ke fitarwa ya ragu a watan Maris. Ta bayyana hakanne a cikin rahoton da ta fitar na watan Afrilu inda tace Najeriya ta samu ragin kaso 4.37 cikin 100 na yawan danyen man fetur din da take fitarwa. Yawan danyen Man Fetur dun ya sauka daga ganga 1.465 da Najeriya ke fitarwa kullun zuwa Ganga 1.401. Hakan dai yayi kasa da yawan man fetur din da kungiyar ta OPEC ke son kowace kasa dake cikin ta ta rika fitarwa na ganga Miliyan 1.5 a kullun. An bayyana matsalolin rashin zuba hannun jari, da Tsaffin kayan aiki da kuma satar danyen man a matsayin abubuwan dake kawo tangarda wajan samun yawan danyen man fetur din da ake bukata.
Kalli Bidiyo:Yanda Barayi suka shiga barikin soji suka saci motoci 3, an kamasu

Kalli Bidiyo:Yanda Barayi suka shiga barikin soji suka saci motoci 3, an kamasu

Duk Labarai
Wasu barayi masu karfin hali sun shiga Barikin soji a kasar Afrika ta kudu inda suka saci wasu motoci. Lamarin ya farune a yankin Thaba Tshwane na kasar Inda aka ga sojoji zagaye da barayin suna musu tambayoyi. https://www.youtube.com/watch?v=v4UgNGf5ncQ Barayin dai sun yi nasarar kutsawa cikin barikin inda suka saci motocin 3. Amma wata tawagar sojoji ta yi saurin kamasu kamin simu tsere.
ACF ta buƙaci ƴan Najeriya su shirya fuskantar ambaliya a bana

ACF ta buƙaci ƴan Najeriya su shirya fuskantar ambaliya a bana

Duk Labarai
Ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya wato ACF ta yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ƴan ƙasar da su fara shirin fuskantar ambaliyar daminar bana. Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a matsayin martani kan hasashen ambaliya ta shekarar 2025 da hukumar kula da yanayi ta fitar, inda a ciki hukumar ta lissafa garuruwa aƙalla 1,249 a ƙananan hukumomi 176 da ke jihohi 30, ciki har da jihohi 16 na arewa za su fuskanta. A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na hukumar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yiwuwar faɗaɗar ambaliyar, da fargabar yadda za ta jawo tsaiko a harkokin rayuwa da walwalar al'umma yankin. Ƙungiyar ta ce ta ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya na wayar da kan al'umma kan batun ambaliyar, amma ta ce ƙoƙarin bai fit...