Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Idan Baku Daukar shawarwarin da muke bayarwa ba za’a kawo karshen matsalar tsaro ba a kasarnan>>Akpabio ya Gargadi Tinubu

Idan Baku Daukar shawarwarin da muke bayarwa ba za’a kawo karshen matsalar tsaro ba a kasarnan>>Akpabio ya Gargadi Tinubu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kakakin majalisar Dattijai ya gargadi bangaren zartaswa akan su daina sukar shawarar da majalisar ke bayarwa kan yanda za'a magance matsalar tsaron kasarnan. Majalisar Dattijai dai ta bayar da shawarar a yi taron karawa juna sani na kwanaki 2 dan samo hanyar da za'a magance matsalar tsaron Najeriya. Saidai Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa ba ta irin hakane za'a kawo karshen matsalar tsaro ba inda yace kwamandojin sojoji ne ke bayar da odar yanda za'a kai ...
Labari Me Dadi: Bankin Duniya ya bayar da Dala Miliyan $215 a rabawa Talakawa kyauta saboda halin matsin da ake ciki

Labari Me Dadi: Bankin Duniya ya bayar da Dala Miliyan $215 a rabawa Talakawa kyauta saboda halin matsin da ake ciki

Duk Labarai
Najeriya ta samu karin bashin dala Miliyan $215 daga bankin Duniya wanda ta nema dan rabawa talakawa tallafi kyauta. Gaba dayan bashin da Gwamnatin Najeriya ta nema dala Miliyan $800 ne wanda tace zata yi amfani dashi wajan rabawa Talakawa kudin kyauta, musamman tsofaffi da masu nakasa da saran masu rauni cikin al'umma. Tun a shekarar 2021 ne Gwamnatin ta nemi bashin saidai saidai bankin Duniyar be bayar da kudin gaba daya ba. Yana bayar dasu da kadan kadanne, zuwa yanzu Bankin ya bayar da Jimullar dala Miliyan $530 kenan. Wannan tallafi dai za'a bayar dashi ne saboda ragewa mutane radadin cire tallafin man fetur dana dala da sauran tsare-tsaren gwamnati da suka jefa mutane cikin halin kaka nika yi.
An garzaya da jirgin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zuwa kasar Afrika ta Kudu dan sake masa fenti da yi mai wasu sauran kwaskwarima

An garzaya da jirgin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zuwa kasar Afrika ta Kudu dan sake masa fenti da yi mai wasu sauran kwaskwarima

Duk Labarai
Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na cewa, an garzaya da jirgin shugaban kasar zuwa kasar Afrika ta kudu dan yi mada fenti da sauran Gyare-Gyare. Wata majiya daga fadar shugaban kasar ce ta bayyanawa kafar Jaridar Punchng haka inda tace za'awa jirgin Fenti ne irin na tutar Najeriya da sauran 'yan Gyare-Gyaren. Rahoton yace zuwa yanzu, an kashe Naira Biliyan N20.03bn waja kula da jiragen shugaban kasar cikin abinda bai wuce shekara guda ba. Jiragen shugaban kasar Najeriya na daya daga cikin manya a Nahiyar Afrika.
Ni ba irin sakarkarun ‘yan siyasar nan bane wanda kawai daga an musu zargin karya sai su sauka daga mukaminsu, Ni ba zan sauka daga kan mukami na ba>>Godswill Akpabio

Ni ba irin sakarkarun ‘yan siyasar nan bane wanda kawai daga an musu zargin karya sai su sauka daga mukaminsu, Ni ba zan sauka daga kan mukami na ba>>Godswill Akpabio

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya bayyana cewa ba zai sauka daga kan mukaminsa ba saboda zarge-zargen karya da ake masa. Ya bayyana hakane bayan da Sanata Natasha Akpoti ke zarginshi da nemanta da lalata sannan kuma Aka zargeshi da aikata magudin zabe. Akpabio yace idan magana ta shiga kotu aka wankeshi ko wa zai gane cewa shi ba me laifi bane.
Kalli Bidiyo: Bamu daga cikin wadanda Kudin mu zasu shiga hannun Bandit da sunan biyan kudin Fansa, idan har tsautsai yasa na shiga hannunsu to zan dauka Allah ya kaddaromin Shahadane ta wannan hanyar>>Sheikh Ibrahim Maqari

Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, irinsu basa daga cikin wadanda kudinsu zasu shiga hannun masu garkuwa da mutane. Malam Yace Allah ya kare amma idan har tsautsai yasa sun shiga Hannun wadannan mutane to zasu dauka cewa, Allah ya kaddaro musu shahadane ta wannan hanyar. https://www.tiktok.com/@habib_habib_jotko/video/7501088179395628343?_t=ZM-8wC7KbRaU1H&_r=1 Da yawa sun yiwa Malam Fatan Allah ya tsareshi.
Kalli Bidiyon yanda wani Kirista ya shiga Masallaci ya samu Liman ya mai karyar shi sabon musulunta ne, yana son a koya masa yadda ake sallah, Ko da Limamin yayi sujada sai ya zaro wuka ya caka mai fiye da sau 40

Lamarin ya farune a kasar Faransa inda wani matashi dan shekaru 20 wanda kirista ne amma ya shiga masallaci yace shi sabon shiga addinin Musukunci ne kuma yananson Limamin Masallacin ya koya masa yadda ake Sallah. Ko da Limamin ya tashi yana Sallah, sai da ya bari ya yi sujada, ya zaro wuka ya caka masa fiye da sau 40. Sunan Limamin Aboubakar Cissé kuma dan Asalin kasar Mali ne. Lamarin ya farune ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata. Kalli Bidiyon anan
DA DUMIDUMINSA: Muna Tare Da Tinubu Dari-Bisa Dari, Inji Tsoffin Membobin Tsohuwar Jam’iyyar CPC Magoya Bayan Buhari

DA DUMIDUMINSA: Muna Tare Da Tinubu Dari-Bisa Dari, Inji Tsoffin Membobin Tsohuwar Jam’iyyar CPC Magoya Bayan Buhari

Duk Labarai
DA DUMIDUMINSA: Muna Tare Da Tinubu Dari-Bisa Dari, Inji Tsoffin Membobin Tsohuwar Jam'iyyar CPC Magoya Bayan Buhari Magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karkashin kungiyar tsohuwar jam’iyyar CPC dake cikin jam’iyyar mai mulki ta APC, wanda Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya jagoranci hira da manema labarai a yau Alhamis sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis. Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar ba sa jin dadin yadda Tinubu ke tafiyar da al’amura, kuma suna shirin ficewa daga jam’iyyar APC gaba ɗaya. Cikin wadanda suka halarci taron a Abuja ranar Alhamis, wadanda kuma suka nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Tinubu, akwai Gwamnan jihar Katsina, D...