Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan majalisar Tarayya sun karawa kansu hutun sati daya

‘Yan majalisar Tarayya sun karawa kansu hutun sati daya

Duk Labarai
'Yan majalisar tarayya da suka hada da Majalisar Dattijai data wakilai sun daga ranar da zasu dawo aiki zuwa 6 ga watan Mayu. 'Yan majalisar a baya sun shirya dawowa bakin aiki ranar 29 ga watan Afrilu saidai yanzu sun karawa kansu sati daya. Wakilin majalisar, Kamoru Ogunlana ne ya bayyana hakan ga sauran 'yan majalisar inda yace an sanar da hakanne saboda baiwa 'yan majalisar damar yin bikin ranar ma'aikata.
Shin da gaske akwai Baraka tsakanin Buhari da Tinubu? Ji bayani dalla-dalla

Shin da gaske akwai Baraka tsakanin Buhari da Tinubu? Ji bayani dalla-dalla

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa da ke Najeriya, Abdullahi Sule ya ce wasu na son yin amfani da rashin "zuwan tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari Abuja" domin nuna cewa akwai ɓaraka tsakaninsa da shugaban ƙasar mai ci, Bola Tinubu. Gwamna Sule ya bayyana haka ne yayin da alamu suka bayyana cewa an samu ɓaraka tsakanin makusantan tsohon shugaban ƙasar, waɗanda suka kasance a jam'iyyar CPC, wadda Buhari ya jagoranta kafin shiga haɗakar da ta samar da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar. A baya-bayan nan wani ɓari na ƴaƴan tsohuwar jam'iyyar ta CPC sun bayyana mubaya'arsu ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, sai dai kwanaki kaɗan bayan hakan wasu ƴaƴan tsohuwar jam'iyyar kuma waɗanda ke da matuƙar kusanci da Buhari sun nesanta kansu daga mubaya'ar. Haka nan sauya sheƙar tsohon gwamnan jihar Kaduna...
Da Duminsa: Fafaroma Francis ya mutu

Da Duminsa: Fafaroma Francis ya mutu

Duk Labarai
Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami'ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya. A shekarar 2023 ne cocin ta zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin.
Yayin da aka yi sati 3 ba’a ga shugaba Tinubu ba, ‘yan Najeriya sun shiga damuwa inda suka tambayar ina shugaban kasar ya shiga ne lafiya kuwa?

Yayin da aka yi sati 3 ba’a ga shugaba Tinubu ba, ‘yan Najeriya sun shiga damuwa inda suka tambayar ina shugaban kasar ya shiga ne lafiya kuwa?

Duk Labarai
Tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tafi kasar Faransa a ranar 2 ga watan Afrilu, fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa zai yi sati biyu ne. Saidai yayin da ake tsammanin zai dawo ranar 16 ga watan Afrilu, shugaban kasar bai dawo ba inda musamman 'yan Adawa suka fara tambayar ba'asi. Fadar shugaban kasar ta sake fitar da sanarwa inda tace shugaban kasar yana nan lafiya kuma yana gudanar da aiki daga can kasar Faransar da yake. Saidai hakan a cewar masana ya sabawa aiki inda bai kamata ace daga kasar Wajene shugaban kasar zai rika gudanar da gwamnati ba. Abubuwan da dama sun faru musamman bangaren matsalar tsaro inda aka yi kashe-kashe amma shugaban kasar bayanan inda daga can kasar Faransa ne ya baiwa jami'an tsaro umarnin cewa su magance matsalar da kakka...
A yau, Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar Filato dan jajantawa iyalan wadanda aka kàshè

A yau, Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar Filato dan jajantawa iyalan wadanda aka kàshè

Duk Labarai
A yau, Litinin, Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar Filato dan jajantawa iyalan wadanda aka kashe a hare-haren da suka faru a jihar. Mutane sama da 100 ne aka kashe a jihar biyo bayan wasu munanan hare-haren da aka kai a cikin makonnin nan. Ministan jinkai da rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda ne ya tabbatar da zuwan mataimakin shugaban kasar a yayin da ya kai ziyara Bassa ranar Asabar dan ganewa idansa yanda lamarin ya faru. Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kansa ne ya baiwa Kashim Shettima umarnin kai wannan ziyara. A yayin ziyarar tasa ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai gana da masu ruwa da tsaki na yankin dan samo hanyar magance wannan matsalar.
Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman Kiristoci suka soki Gwamnatinsa

Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman Kiristoci suka soki Gwamnatinsa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman kiristoci, Bishop Matthew Hassan Kukah da Pastor Tunde Bakare suka soki Gwamnatinsa. A sakonsu na bikin Easter, Manyan malaman kiristocin sun nemi shugaban kasar ya dauki matakai akan matsin tattalin arziki da matsalar tsaro da ake fama da ita. Saidai da yake mayar da martani ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala, shugaba Tinubu yace a wasu bangare da Fasto Tunde Bakare ya sokeshi sun sha banban amma kuma yana da 'yanci a matsayinsa na dan kasa ya bayyana ra'ayinsa. Yace amma shugaban kasar ya mayar da hankali wajan ganin ya cika alkawuran da ya daukarwa 'yan Najeriya.
Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga ta hanyar karbar kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 14

Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga ta hanyar karbar kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 14

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga daga kudaden ruwa da suke karba a hannun wadanda suka baiwa bashi da suka kai Naira Tiriliyan 14.26. Hakan ya bayyana ne bayan kammala kididdigar da aka yi ta kudaden shigan bankunan a shekarar 2024. Bankunan da suka samu wadannan kudaden shigar sune, Fidelity, UBA, GT Bank, First Bank, Wema Bank, Stanbic IBTC, FCMB, Access, da Zenith Bank. Rahoton yace a shekarar 2023 bankunan sun samu kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 6.49 wanda idan aka hada da kudaden ruwan da suka samu a shekarar 2024 na Tiriliyan 14.26, hakan na nufin sun samu karin kaso 119.55 cikin dari kenan na kudin ruwan. Saidai a gefe guda, yayin da bankunan ke murnar samun kudin ruwa daga hannun wadanda suka baiwa bashin, su kuma wadanda suka k...
Ji yanda ‘Ƴàn bìndìgà ke ci gaba da ɗora wa al’umma haraji a Zamfara

Ji yanda ‘Ƴàn bìndìgà ke ci gaba da ɗora wa al’umma haraji a Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun saka harajin miliyoyin naira ga wasu al'umomi da ke yankin Ɗan Kurmi a ƙaramar hukumar mulki ta Maru. Ƴanbindigar sun ayyana Laraba a matsayin ranar wa'adin biyan kuɗin amma tuni suka fara aiwatar da dokar tsare mutane a garin Zargado har sai an biya kudin a matsayin diyya. Al'ummar yankin da abin ya shafa sun sheda wa BBC cewa sun samu kansu a wannan tasku ne bayan da wasu mazauna yankin suka kona daji da kuma hare-haren da sojoji suka kai wa 'yanbindigan shi ne barayin dajin suka dora musu wannan haraji na naira miliyan 60. Honarabul Iliyasu Salisu Dankurmi ya tabbatar wa da BBC wannan lamari : ''Sojoji sun shigo aiki wannan yanki sun koma to kuma yanzu 'yanbindiga sun zo sun aza mana haraji, suka ce sai ...
Kalli Bidiyon yanda Gobara ta tashi a wajen sayar da Gas a Rijiyar Zaki Kano, Ji yanda Tukwanen Gas suka rika fashewa suna kara kamar Bàm

Kalli Bidiyon yanda Gobara ta tashi a wajen sayar da Gas a Rijiyar Zaki Kano, Ji yanda Tukwanen Gas suka rika fashewa suna kara kamar Bàm

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an samu fashewar tukunyar gas a wani wajan sayar da gas din dake Dorawar 'yan Kifi, Rijiyar Zaki. A bayanan da hutudole ya samu shine ba'a samu asarar rayuka ko jikkata ba saidai asarar Dukiya. A bidiyon da suka rika yawo a kafafen sada zumunta, an ga da jin yanda tukwanen gas din duka rika fashewa kamar bam na tashi. https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495415482929974583?_t=ZM-8vhcbEDH8TN&_r=1 https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495418146510179639?_t=ZM-8vhcgdjSPDT&_r=1 https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495422464655101189?_t=ZM-8vhcl2xDLao&_r=1 https://www.tiktok.com/@a.k.a.i.s.u/video/7495433889079463174?_t=ZM-8vhcsqiCr3O&_r=1 Saidai daga baya 'yan kwana-kwana sun kai wajan sun kashe gobara...
Kiran mutane su tashi tsaye su kare kansu bashine mafita ba ga matsalar tsaro>>Bulama Bukarti ya mayarwa da T.Y Danjuma Martani bayan da yace mutane su tashi tsaye su kare kansu Gwamnati ba zata iya ba ita kadai

Kiran mutane su tashi tsaye su kare kansu bashine mafita ba ga matsalar tsaro>>Bulama Bukarti ya mayarwa da T.Y Danjuma Martani bayan da yace mutane su tashi tsaye su kare kansu Gwamnati ba zata iya ba ita kadai

Duk Labarai
Babban me sharhi akan Al'amuran tsaro, Bulama Bukarti ya mayarwa da Tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma martani kan kiran da yayi mutane su tashi tsaye su kare kansu game da matsalar tsaro. T.Y Danjuma yace gwamnati ba zata iya ba ita kadai inda yace kamata yayi mutane su tashi su kare kansu. Saidai a hirar da aka yi dashi a Channels TV, Bulama Bukarti ya bayyana cewa wannan ba mafita bace. Yace idan aka yi hakan, makamai zasu karu a hannun farar hula wanda hakan zai kawo ci gaba da kisan mutane ba tare da hukunci ba.