Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Fararoma yayi kiran a yi Sulhu a Gaza

Fararoma yayi kiran a yi Sulhu a Gaza

Duk Labarai
Babban Limamin Kirista, Fafaroma Francis ya nemi a yi sulhu a yakin da ake tsakanin kungiyar Hamas da Israela. Yayi wannan kirane a yayin da ake bukukuwan Easter. Yawan wanda aka kashe a Falasdin ya haura mutane dubu 50 ciki hadda mata da kananan yara. Fafaroma ya kuma bayyana a karin farko tun bayan da yayi doguwar rashin lafiya a bainar jama'a. Hakanan Mataimakin shugaban kasar Amurka, J.D Vance ya halarci fadar Fafaroman yayin da ake bukukuwan Easter.
Najeriya ta mayar da ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba

Najeriya ta mayar da ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba

Duk Labarai
Hukumar shige da fice ta Najeriya ta tabbatar da mayar da wasu ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Cikin wata sanarwar da babban kwanturolan hukumar mai lura da kan iyakar Illela - inda ta nan ne aka fitar da mutanen - Tony Akuneme ce mutanan sun haɗa da maza 51 da kuma mata 11, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar, NAN ya ruwaito. Mista Akuneme ya ce jami'an hukumar ne suka yi wa mutanen rakiya daga shalkwatar hukumar shige da fice ta ƙasa da ke Abuja zuwa kan iyakar Illela da ke jihar Sokoto, cikin motocin bas biyu. Ya ƙara da cewa bayan tanatance takardunsu, an miƙa su ga jami'an ƴansandan Nijar da ke Birnin Konni. A baya-bayan nan Najeriya mayar da ƴan ciranin da ke shiga ƙasar daga maƙwabtan ƙasashe ba tare da cikakkun takardun izini ba. A watanni...
Rashin Wutar Lantarki na Kwanki 10 a jihar Kano ya gurgunta harkokin tattalin arzikin jihar inda Cajin waya yanzu ana karbar Naira 200, jarkar ruwa ma ta koma Naira 200

Rashin Wutar Lantarki na Kwanki 10 a jihar Kano ya gurgunta harkokin tattalin arzikin jihar inda Cajin waya yanzu ana karbar Naira 200, jarkar ruwa ma ta koma Naira 200

Duk Labarai
Rashin tsayayyiyar wutar lantarki na tsawon lokaci na sama da kwanaki 10 ya jawo dakatar da kasuwanci a cikin ƙwaryar birnin Kano da kewaye. Wasu mazauna Kano da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Lahadi, sun koka game da rashin sanin tabbacin abin da za su yi bayan faɗuwar babban layin wutar lantarki wanda ya jefa al’umma cikin duhu da shafar kasuwanci da al’umma a gidajensu. Da yawa daga cikin ‘yan kasuwa sun koka game da illar rashin wuta ga kasuwancinsu. Wani mai gidan otel da unguwar Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fage, Jude Michael, ya ce yana cikin tashin hankali. Michael ya ce ya rasa kwastamominsa sakamakon rashin wuta da yake amfani da ita wajen ajiye kayan abin sha. “Na shafe tsawon kwanaki ina aiki da Janareta kuma har ya fara taɓa k...
‘Yan Bìndìgà sun tare motar Bas cike da mutane suka sàcèsù akan hanyar Malunfashi zuwa Funtua

‘Yan Bìndìgà sun tare motar Bas cike da mutane suka sàcèsù akan hanyar Malunfashi zuwa Funtua

Duk Labarai
'Yan Bindiga a daren ranar Alhamis sun tare wata Motar Bas inda suka sace mutanen cikinta su duka. Motar dai na tafiyane akan Titin Malunfashi zuwa Funtua. Rahoton yace lamarin ya farune a daidai kauyen Burdugau kamar yanda me amfani da kafar X, Bakatsine ya bayyana. Saidai zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukumomi game da lamarin.
Fati Karishma Kenan, Wadda A Shekarun Baya Kaf Masana’antar Finafinan Hausa Ba Wacce Ta Kai Ta Iya Rawa

Fati Karishma Kenan, Wadda A Shekarun Baya Kaf Masana’antar Finafinan Hausa Ba Wacce Ta Kai Ta Iya Rawa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Fati Karishma Kenan, Wadda A Shekarun Baya Kaf Masana'antar Finafinan Hausa Ba Wacce Ta Kai Ta Iya Rawa Ko kun tuna ta?
Ba wai Lusarin Mataimakin Gwamnan da bashi da katabus a jihar Bauchi ba, wallahi ko Gwamnan Bauchi ya sake ya mari babana da sai Babana ya faffasa mai baki da hanci>>Inji Dan Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar inda yace karyane ba’a mari babansa ba

Ba wai Lusarin Mataimakin Gwamnan da bashi da katabus a jihar Bauchi ba, wallahi ko Gwamnan Bauchi ya sake ya mari babana da sai Babana ya faffasa mai baki da hanci>>Inji Dan Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar inda yace karyane ba’a mari babansa ba

Duk Labarai
Dan Ministan harkokin kasashen waje, Adam Tuggar ya musanta rahoton dake cewa mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Jatau ya mari babansa. Rahotanni dai sun bayyana cewa dan Gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed ne ya yada wannan labari a shafinsa na sada zumunta. Da yake mayar da martani, Adam Tuggar ya bayyana Shamsuddeen a matsayin wanda bashi da tarbiyya wanda kuma shi da babansa sun yi zaman gidan yari kamin baban nasa ya zama Gwamna. Sannan yace wannan dabi'a da yake nunawa a wajen mahaifinsa ya gajeta. Yace shi baya shiga irin wannan lamari amma tunda an taba babansa, dole ya fito ya kareshi. Yace Shamsuddeen Ya saba yiwa manyan mutane irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar rashin kunya saboda kawai su na da banbancin ra'ayi da mahaifinsa. ...
Kalli Hoto: Yanda aka kama sojan Najeriya, Yahya Yunusa na safarar makamai a Kaduna

Kalli Hoto: Yanda aka kama sojan Najeriya, Yahya Yunusa na safarar makamai a Kaduna

Duk Labarai
An kama karamin sojan Najeriya me suna Private Yahaya Yunusa a Jaji dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna saboda zargin safarar makamai. Sojan dake aiki a bataliya ta 197 dake jihar Zamfara an kamashine ranar Juma'a da misalin karfe 11:55 a.m. inda aka samu albarusai 214 a wajensa. An kuma kamashi da ATM da yawa. Ya amsa laifinsa inda yace ya saci albarusanne daga wajen aikinsa dan shine ke kula da bindigar A.A da ake kafewa a bayan motar yakin sojoji.
Kalli Yanda aka kama Hòdàr Iblis Boye a cikin litattafan Addini za’a kaita kasar Saudiyya daga Najeriya

Kalli Yanda aka kama Hòdàr Iblis Boye a cikin litattafan Addini za’a kaita kasar Saudiyya daga Najeriya

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama kulli 20 na hodar iblis da aka boye a tsakanin litattafan addini da za'a yi safararta zuwa kasar Saudiyya. Shugaban hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. Yace an yi kamenne ranar 15 ga watan Afrilunnan da muke ciki, saidai bai bayar da karin haske kan ko an kama wadanda suka yi yunkurin aikata wannan laifi ba.
Kalli yanda aka kama sojan Najeriya da fashi da makami da satar mota

Kalli yanda aka kama sojan Najeriya da fashi da makami da satar mota

Duk Labarai
Hukumomin 'yansanda sun kama Sojan Najeriya da ake zargi da satar mota. Sojan ya hada kai da wani farar hula ne dan satar mota kirar Toyota Hilux a garin Legas. An kama su biyunne a yayin da suke kokarin kai motar da suka sata zuwa kudancin Najeriya. Sojan dake aiki a rundunar Operation Delta Safe dake jihar Bayelsa, ya bi dayan farar hular ne dan ya rika nuna ID card dinsa na aikin sojane ana barinsu suna wuce shingen jami'an tsaro. Saidai 'yansanda sun bi sahunsu suka kamasu a yayin da suke kokarin kai motar inda zasu sayar
Buhari ne ya gina ramin da Tinubu ya jefa mu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa Hakeem Baba Ahmad

Buhari ne ya gina ramin da Tinubu ya jefa mu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa Hakeem Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya haka ramin da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jefa 'yan Najeriya ciki. Ya bayyana hakane a wata ganawa ta musamman da aka yi dashi tun bayan da ya ajiye aikin nasa. Yace Shugaba Buhari ya taba cewa jiki Magayi yace a yanzu ne ma ya kamata a fadi wannan kalma. Yace nan da watanni 6 za'a kafa wata tafiya wadda zata jagoranci inda Arewa zata fuskanta.