Sunday, March 29
Shadow

Author: Bashir Ahmed

YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas Ya Janye Kudirin Tilasta Zaɓe wanda za’a rika cin mutum tarar Naira dubu dari bayan da ya sha suka

YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas Ya Janye Kudirin Tilasta Zaɓe wanda za’a rika cin mutum tarar Naira dubu dari bayan da ya sha suka

Duk Labarai
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya janye kudirin dokar da ke neman tilasta wa 'yan Najeriya kada kuri'a a kowane zaɓe. Kudirin dai na neman gyara Dokar Zaɓe ta 2022, inda aka tanadi cewa duk masu cancantar kada kuri’a dole ne su fito su zaɓa a kowanne zabe, kuma wanda ya ki, zai iya fuskantar hukunci na daurin watanni shida zuwa tara, ko tara har Naira 100,000. Sai dai, wannan kudiri ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan adam. Kungiyar SERAP ta bayyana cewa wannan yunkuri ya sabawa yancin dan adam, kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa da kasa. Sun jaddada cewa 'yancin kada kuri’a yana nufin mutum na da damar yanke shawara – ya kada kuri’a ko kuma ya ki. Haka kuma, sun yi barazanar daukar matakin shari’a idan aka amince da kudirin. Fi...
Iyalina sunce matsin Yayi Yawa in Aje Mukamina Kada A Kàshè ni, Kamar Yanda Aka Kèshè Thomas Sankara: Nace Masu A A Koda na Mùtù To Tabbas Na Mùtù ne Wurin ceto Al’ummar mu>>Inji Matashin Shugaban kasar Burkina

Iyalina sunce matsin Yayi Yawa in Aje Mukamina Kada A Kàshè ni, Kamar Yanda Aka Kèshè Thomas Sankara: Nace Masu A A Koda na Mùtù To Tabbas Na Mùtù ne Wurin ceto Al’ummar mu>>Inji Matashin Shugaban kasar Burkina

Duk Labarai
Iyalina sunce matsin Yayi Yawa in Aje Mukamina Kada A Kashe ni, Kamar Yanda Aka Kashe Thomas Sankara: Nace Masu A A Koda na Mutu To Tabbas Na Mutu ne Wurin ceto Al'ummar mu. Shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Traore Tabbas Kowa Yasan Akwai Kalubale Mai Yawa A Gaban Sa, A Halin Yanzu Kawai Muna Yimasa Addua Allah Ya kara Bashi Kariya.
Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta kulle ofishin hukumar karbar Haraji ta kasa, FIRS, da bankin Access Bank, da gidan Man Total da sauransu saboda rashin biyan Haraji

Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta kulle ofishin hukumar karbar Haraji ta kasa, FIRS, da bankin Access Bank, da gidan Man Total da sauransu saboda rashin biyan Haraji

Duk Labarai
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta kulle matan gine-gine a birnin saboda rashin biyan kudaden haraji da ake binsu. Wasu daga cikin manyan gine-ginen da aka kulle sun hada da: Babban Ofishin Jam'iyyar PDP na kasa. Ofishin hukumar tattara Haraji na kasa, FIRS dake Zone 5. Ofishin Access Bank dake Wuse. Da ofishin al'adun kasar China dake Zone 5. Da gidan man Total dake Zone 5. Da dai sauransu.
Hotuna: Wasu da ba’a san ko su wanene ba sun Kònà ofishin ‘yansanda a Rano dake Kano, Mutum daya ya mùtù

Hotuna: Wasu da ba’a san ko su wanene ba sun Kònà ofishin ‘yansanda a Rano dake Kano, Mutum daya ya mùtù

Duk Labarai
Hotuna: Kwamishinan yan sandan Kano ya ziyarci ofishin yan sanda da aka kona a Rano. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, tare da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Hon. Mallam Mohammed Naziru Ya’u, sun kai wata ziyara ta gaggawa domin tattara bayanai kai tsaye a caji ofis din ‘yan sanda na Rano da ke Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano. Ziyarar na zuwa ne sakamakon mummunan hari da wasu da ba a tantance ba suka kai a safiyar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da lalata wasu sassa na ofishin ‘yan sanda a Rano. Kwamishinan ‘Yan Sanda ya ce wannan ziyara na cikin matakan bincike da tabbatar da tsaro a yankin. Ya kuma jaddada cewa rundunar ‘yan sanda tana daukar duk matakan da suka dace domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika da da...
Ana fargabar ƴan bindiga sun sace mutane da dama a Abuja

Ana fargabar ƴan bindiga sun sace mutane da dama a Abuja

Duk Labarai
Wasu masu garkuwa da mutane dauke da makamai sun kai farmaki unguwar Grow Homes da ke cikin yankin Chikakore na Kubwa – wacce ita ce mafi girma cikin unguwannin da ke wajen birnin Abuja – da safiyar Litinin, inda suka yi garkuwa da mazauna unguwar. Jaridar Vanguard ta rawaito daga bakin wasu mazauna unguwar da abin ya firgita cewa lamarin ya faru tsakanin karfe 12 na dare zuwa karfe 1:30 na dare. Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da ganin wani namiji da wata mace suna cikin wadanda aka sace, ya ce da safiya an sami matar a cikin unguwar, bayan da masu garkuwar suka sako ta ba tare da bayani ba. Sai dai bai tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba. “Lamarin ya faru kusan karfe 12 na dare. Wadannan mutane sun zo da makamai sosai, sun kuma fi karfin kungiyar tsaron sa-kai. ‘Yan...
Kotu ta yanke hukuncin kìsà ga matashin da ya kona masallata a Kano

Kotu ta yanke hukuncin kìsà ga matashin da ya kona masallata a Kano

Duk Labarai
Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano. Babbar Kotun Shari’a da ke Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mutum da ya kunna wuta a cikin wani masallaci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane da kuma jikkatar da dama. Lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayu, 2024, a kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano. Mai shari’a Halhatu Huza’i Zakariyya ne ya yanke hukuncin bayan ya samu wanda ake tuhuma da laifuka hudu da suka shafi kashe-kashe da haddasa munanan raunuka. Kotun ta bayyana cewa laifin da aka aikata ya saba wa doka, kuma hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da laifin mutumin ba tare da tantama ba.
Ji Dalilin da yasa Kasar Saudiyya ta hana Sheikh Dr. Ahmad Gumi yin aikin Hajjin bana, kamar yanda yayi karin bayani

Ji Dalilin da yasa Kasar Saudiyya ta hana Sheikh Dr. Ahmad Gumi yin aikin Hajjin bana, kamar yanda yayi karin bayani

Duk Labarai
Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana babban malamin addinnin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin hajjin bana. Sheikh Gumi wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnatin Saudiyya bayan ta ba shi bizar shiga ƙasar domin aikin Hajji amma kuma sai ba a ba shi damar shiga Madina domin fara aikin ibada ba. "Bisa waɗansu dalilai saboda ra'ayi na kan siyasar duniya, hukumomi a Saudiyya ba sa son kasancewata a Hajji duk da sun ba ni biza," in ji Sheikh Gumi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ya ƙara da cewa "Ina godiya ga hukumomi a Najeriya waɗanda suka sha alwashin tuntuɓar hukumomin Saudiyya a kan wannan lamarin." Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na cikin tawagar malaman da hukumar aikin hajjin...