Sunday, March 29
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Hankula sun tashi bayan da aka dauke wutar lantarki a kasar Faransa na tsawon awanni 5

Hankula sun tashi bayan da aka dauke wutar lantarki a kasar Faransa na tsawon awanni 5

Duk Labarai
Rahotanni daga birnin Riviera na kasar Faransa inda ake bikin fina-finai na kasa da kasa na cewa, an dauke wuta na tsawon akalla awanni 5. Hakan ya kawo tarnaki a bikin finafinan da ake yi inda baki da dama da suka je wajan bikin ke kokawa musamman game da maganar kudi da zasu yi hidima dasu saboda bankuna da ATM duk sun samu tangarda saboda rashin wutar. Rahotanni sun ce wasu bata garine suka lalata kadarorin wutar lantarkin wanda hakan ya kawo tarnaki aka dauke wutar. Lamarin ya zowa mutane da mamaki ganin kasa me ci gaba irin Faransa ta samu matsalar wutar lantarki haka.
ASUU ta yi barazanar tafiya yajin aiki da rufe jami’o’in Najeriya

ASUU ta yi barazanar tafiya yajin aiki da rufe jami’o’in Najeriya

Duk Labarai
Ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta cika yarjejeniyar da suka shiga a shekarar 2009 ko ta tsunduma yajin aiki. Shugaban ASUU, Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma'a a Abuja. Ya nanata buƙatar da ke akwai na gwamnatin ta cika yarjejeniyar da alƙawuran da ta ɗauka domin magance matsalolin da jami'o'in ƙasar ke fuskanta. Piwuna ya ce har yanzu akwai wasu muhimman batutuwa guda tara da ba a daddale su ba a yarjejeniyar da suka shiga. Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa daga cikin abubuwan da suka rage akwai albashin malaman da ba a biya ba lokacin da suke yajin aiki na shekarar 2022 da wasu alawus ɗinsu da ake riƙe saboda IPPIS da sauransu. Ya ce duk da alƙawarin da gwamnati ta yi na zuba...
Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da yanda ake kirkiro Bidiyo na bogi na shugaban kasa dake nunashi a wani yanayi mara kyau domin ɓata masa suna

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da yanda ake kirkiro Bidiyo na bogi na shugaban kasa dake nunashi a wani yanayi mara kyau domin ɓata masa suna

Duk Labarai
Ministan yaɗa labaran Najeriya Mohammed Idris ya gargaɗi ƴan ƙasar kan amfani da ƙirƙirarrun bidiyo domin nuna shugabannin ƙasar a wani yanayi mara kyau domin ɓata musu suna. Jaridar The Nation mai zaman kanta ta ruwaito ministan yana cewa, "mun ga yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira ta hanyoyin da suka dace, da hanyoyin da ba su dace ba. Zai iya yiwuwa kana zaune a nan kawai sai wani ya yanko kanka ya ɗaura a wani jikin domin ɓata maka suna." "Muna ganin yadda ake juya maganar shugaban ƙasa, inda zai faɗa abu daban, amma sai a canja abin da ya faɗa. Ko kuma minista ya faɗa wani abu, sai a juya masa magana," in ji shi. Ya ƙara da cewa suna duba lamarin sosai a matakin gwamnati, "musamman yadda za mu tsaftace kafofin sadarwa ba tare da tauye haƙƙin furta albarkacin baki ba."...
Mun ba ɗaliban Najeriya rancen naira biliyan 56.85 a shekara ɗaya – Gwamnatin Tarayya

Mun ba ɗaliban Najeriya rancen naira biliyan 56.85 a shekara ɗaya – Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Hukumar Bayar da Bashin Karatu ta Najeriya Nelfund ta ce ta ba ɗaliban Najeriya rancen kuɗi naira biliyan 56.55 domin biyan kuɗin makaranta da alawus ɗin kashewa na yau da kullum. Hukumar ta bayyana haka ne domin bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekara ɗaya da fara aiki tun bayan ƙirƙirar shirin. A wata sanarwa da daraktan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi ta fitar, ya ce sama da ɗalibai 600,000 ne suke nami rancen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. "Bayan tantancewa, mun amince tare da ba ɗalibai 550,000 rancen, inda muka ba su kuɗi naira biliyan 56.85 a cikin shekara guda." "Tsarin bayar da rancen ya taimaka wajen sauƙaƙa wa ɗaliban Najeriya da iyaye," in ji ta.
Tinubu Akwai Zalamar Mulki, Yanzu duk wahalar rayuwa da matsalar tsaro da sauransu da ‘yan Najeriya ke ciki bai dameshi ba, zarcewa akan kujerar mulki ce a gabanashi? Inji Jam’iyyar PRP

Tinubu Akwai Zalamar Mulki, Yanzu duk wahalar rayuwa da matsalar tsaro da sauransu da ‘yan Najeriya ke ciki bai dameshi ba, zarcewa akan kujerar mulki ce a gabanashi? Inji Jam’iyyar PRP

Duk Labarai
Daya daga cikin jam'iyyun adawa a Najeriya wato PRP, ta yi alawadai da amincewar da kwamitin zartarwa na kasa na jam'iyyar APC mai mulki, da gwamnonin jam'iyyar, da 'yan majalisar dokoki na kasa na jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki suka yi wa shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu, domin ya sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara ta 2027. Jam'iyyar PRP ta bayyana fargabar, cewa wannan mataki wata zalamar mulki ce kawai, wadda ta fayyace aniyar jam'iyyar APC ta neman ci gaba da mulki karfi da yaji ta hanyar wani goyon baya na musamman da aka tsara, maimakon a bari jama'ar kasa su bayyana ra'ayinsu game da takarar shugaban kasar a zaben da ke tafe. Kwamred Muhammed Ishak, shi ne sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PRP, ya shaida wa BBC cewa sanin kowa ne ba wani dad...
Mutanen mu basu da wayau, kudi ake basu suna zaben gurbatattun shuwagabanni>>Inji Dan siyasar jihar Ekiti

Mutanen mu basu da wayau, kudi ake basu suna zaben gurbatattun shuwagabanni>>Inji Dan siyasar jihar Ekiti

Duk Labarai
Dan siyasar jihar Ekiti wanda kuma dan uwa ne ga tsohon gwamnan jihar, Isaac Fayose ya caccaki mutanen jiharsa. Ya bayyana su da marasa wayau inda yace ana basu kudi kalilan suna zaben gurbatattun 'yan siyasa. Yace bayan zabe haka zaka ga sun koma mabarata. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1925900839316574614?t=IFhtaDTEjlrZw-n1W-tH4w&s=19 Maganar tashi ta jawo cece-kuce sosai inda mutanen jihar suka bayyana rashin jin dadinsu, saidai yace shi har yanzu yana nan kan bakarsa.
Kalli Bidiyo Gwanin ban Tausai: Yanda Dansanda ya fada katon Ramin Kwata a yayin da yake bin me mashin

Kalli Bidiyo Gwanin ban Tausai: Yanda Dansanda ya fada katon Ramin Kwata a yayin da yake bin me mashin

Duk Labarai
Wannan wani Dansanda ne da ya dauki hankulan mutane. Rahotanni sun ce yana bin wani me achaba ne inda ya fada cikin Kwata me Zurfi. Lamarin ya farune a Legas inda daga baya mutane suka zura mai kuranga ya fito. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1924802928574890479?t=gJMkW8_RjnXVcW_7k1S8Gg&s=19 https://www.youtube.com/watch?v=ROSgUg7-82I?si=cJy6C3ptpxSRhV86 Wasu dai sun jajanta masa inda wasu suka mai dariya.
Shekarata 31 a masana’antar Fim amma babu wanda na yadda ya taba yin lalata dani

Shekarata 31 a masana’antar Fim amma babu wanda na yadda ya taba yin lalata dani

Duk Labarai
'Yar fim din kudi, Thelma Chukwunwem ta bayyana cewa shekararta 31 tana fim amma babu wani darakta ko Frodusa da zai ce ya taba kwanciya da ita. A hirar da aka yi da ita a Jaridar Vanguard tace a lokacin da ta fara fim an ta kai mata harin neman yin lalata da ita amma ta ki yadda. Tace akwai daraktan da ya taba gaya mata ba zata ci gababa tunda bata basu hadin kai amma ita ta bashi amsar cewa Allah zai taimaketa. Ta alakanta hakan da tarbiyyar data samu a gida.
Watanni Biyu Da Suka Wuçe Na Yi Ta Cin Kaŕo Da Yaran Bèĺlo Tùrjì A Saudiyya Sun Jè Yìn Umrah, Har Sukè Yi Min Bàrazanar Cewa Na Yi Sa’a Ba A Nijeŕiya Muka Hadu Ba, Da Suñ Yi Maganìna Saboda Yadda Nake Yawan Sukàr Ubangidansu, Inji Abba Zango

Watanni Biyu Da Suka Wuçe Na Yi Ta Cin Kaŕo Da Yaran Bèĺlo Tùrjì A Saudiyya Sun Jè Yìn Umrah, Har Sukè Yi Min Bàrazanar Cewa Na Yi Sa’a Ba A Nijeŕiya Muka Hadu Ba, Da Suñ Yi Maganìna Saboda Yadda Nake Yawan Sukàr Ubangidansu, Inji Abba Zango

Duk Labarai
Watanni Biyu Da Suka Wuçe Na Yi Ta Cin Kaŕo Da Yaran Bèĺlo Tùrjì A Saudiyya Sun Jè Yìn Umrah, Har Sukè Yi Min Bàrazanar Cewa Na Yi Sa'a Ba A Nijeŕiya Muka Hadu Ba, Da Suñ Yi Maganìna Saboda Yadda Nake Yawan Sukàr Ubangidansu, Inji Abba Zango