An gurfanar da wata mata Harira Muhammad a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office a jihar Kano, bisa zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda
Ita dai Hariri ta kwashe tsawon watanni 6 basa zaune waje ɗaya da mijinta na farko Sagiru Shuaibu Tudun Murtala, sai dai ya ce ranar da ya ziyarci gidanta, ya tarar da ita kwance a gadonsu na aure da wani, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa.
A lokacin da ta ke kare kanta game da zargin da mijinta na farko ya yi, Hariri ta musanta cewa akwai igiyar aure tsakaninta da shi, amma sai dai da alkalin kotun mai shari'a Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki ya umarce ta data yi rantsuwa da Al-Qur'ani sai ta janye kalamanta.
Shi kuwa a nasa ɓangaren, Bello Abdullahi Ƴankaba mijin Harira na biyu, ya shaida wa kotun cewa ya aureta ne a hannun kawunta Abdullahi Umar kan sadaki naira dubu ɗari.
Bayan kammala jin dukkanin ɓangarorin, mai shari'a Khadi Munzali Tanko...








