Sunday, March 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Wata Budurwa ta kàshè kanta saboda damuwar rayuwa a Abuja

Wata Budurwa ta kàshè kanta saboda damuwar rayuwa a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, wata budurwa ta kashe kanta. Lamarin ya farune a rukunin gidaje na CITEC dake Life Camp, babban Birnin Tarayya, Abuja ranar April 22, 2025. An iske matar da misalin karfe 7:00 a.m. rataye a jikin wata kwantena inda 'yansanda suka isa wajen suka tafi da ita zuwa FMC Jabi inda a canne likitoci suka tabbatar da ta mutu. An dai gano wayarta sannan an fara bincike kan lamarin.
2027: Baba-Ahmed Ya Bukaci Tinubu Ya Janye, Ya Bar Matasa Su Yi Takara 

2027: Baba-Ahmed Ya Bukaci Tinubu Ya Janye, Ya Bar Matasa Su Yi Takara 

Duk Labarai
2027: Baba-Ahmed Ya Bukaci Tinubu Ya Janye, Ya Bar Matasa Su Yi Takara. Tsohon mashawarcin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya hakura da shirin neman tazarce, ya bai wa matasa dama su yi takara domin ciyar da kasa gaba a babban zabe na 2027. A wata budaddiyar wasika da ya aike wa Daily Trust a ranar Laraba, Baba-Ahmed ya roki Tinubu da ya yi watsi da duk wani shirin sake tsayawa takara a 2027. Baba-Ahmed ya bayar da hujjar cewa, Tinubu ya ajiye son ransa, ya bar matasa a mulki, ya fice daga Siyasa a mutunce, shi ne dattaku da barin baya da kyau. “Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi. ...
Shawarar da kuke baiwa shuwagabannin mu na jefa mutane cikin talauci da Yunwa>>NLC ta gayawa IMF

Shawarar da kuke baiwa shuwagabannin mu na jefa mutane cikin talauci da Yunwa>>NLC ta gayawa IMF

Duk Labarai
Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta gayawa kungiyar bada Lamuni ta Duniya IMF cewa shawarwarin gyara da suke baiwa shuwagabannin Najeriya na jefa mutane cikin halin kaka nikayi. NLC ta gayawa IMF hakane a yayin da wakilan IMF din suka zo Najeriya suka je ofishin NLC dan su ji yanda ake ciki game da irin abinda 'yan Najeriya ke cewa kan tsare-tsaren gwamnati. Wakilan IMF biyu, Christian H. Ebeke da Axel Schimmelpfennig ne suka wakilci kungiyar zuwa ofishin NLC. Sun bayyana cewa, IMF tana bayar da shawara ne kawai, bata tursasa kasashe amfani da shawarwarin da take basu. Sannan sun ce mafi yawanci kasashe basa aiwatar da shawarwarin IMF din yanda ya kamata. A nasa bangaren shugaban NLC Joe Ajaero ya bayyana cewa tsare-tsare irin su cire tallafin mai wanda dama can babu shi kawai ...
Na gama da Atiku, Har mataimakinsa Okowa ya dawo APC>>Inji shugaba Tinubu

Na gama da Atiku, Har mataimakinsa Okowa ya dawo APC>>Inji shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ya gama da babban dan Adawa, Atiku Abubakar saboda har wanda yayi masa mataimaki a zaben shekarar 2023, Ifeanyi Okowa ya koma jam'iyyar su ta APC. Ya bayyana cewa ko gamayyar da suke hadawa a yanzu ta watse. Inda ya karkare da cewa, Ya sake yin nasara akan Atiku Abubakar. A jiyane dai Ifeanyi Okowa ya koma jam'iyyar APC daga PDP
A kama Fasto da ya dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki, ya amsa laifinsa

A kama Fasto da ya dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki, ya amsa laifinsa

Duk Labarai
A jihar Ondo Hukumomi na binciken wani fasto me suna Peter James saboda zargin dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki. Yarinyar dai na daya daga cikin mas wake-wake a cocinsa. Lamarin ya farune a garin Oke-Gburowo, dake karamar hukumar Odigbo, ta jihar. Da farko dai jami'an Amotekun ne suka kama faston inda aka kaishi fadar sarkin garin kuma bayan gabatar masa da zargin da ake masa, ya amsa laifinsa Saidai daga baya ya murzawa idanunsa kwalli yace cikin ba nashi bane. Mahaifiyar yarinyar me suna Mrs. Victoria Bernard tace faston ya ki amsa laifinsa ne saboda yaga yarinyar na da nakasa. Ta yi kira ga hukumomi da su amsar musu 'yancinsu.
Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya

Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya

Duk Labarai
Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya. Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Plateau da Benue da kuma Kwara. Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, inda suka yi nazari a kan yanayin tsaro a Najeriya. A wata sanarwa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyan, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwa kan kisan ƴan Najeriya da basu ji ba, ba su gani ba a sassan ƙasar. Shugaban ƙasan wanda ya shafe fiye da sa'oi biyu yana ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, ya ce dole ne su kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar. Sanawar ta ayyano shugab...
Kalli Bidiyo Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da’awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin

Kalli Bidiyo Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da’awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin

Duk Labarai
Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da'awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin. https://www.tiktok.com/@mbabanislam/video/7496294294630731041?_t=ZM-8vmgnwzOzDD&_r=1 A kwanannan ne dai aka ga malaman sun je Da'awa kasashen Turai inda wani Bidiyo ya nunasu a kasar Faransa.
Kalli Bidiyo: An zargi dan Bello da kin biyan matasa hakkokinsu bayan sun masa aiki

Kalli Bidiyo: An zargi dan Bello da kin biyan matasa hakkokinsu bayan sun masa aiki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Bidiyo ya bayyana inda ake zargin shahararren me watsa labarai ta kafafen sadarwa Dan Bello da kin biyan wasu matasa hakkokinsu bayan sun masa aiki. Dan Bello kamar yanda aka ji a bidiyon yayi amfani da matasanne wajan kaiwa kwastomominsa kayayyakin da suka saya a hannunsa. Saidai bayan da suka kammala masa aiki suka ji shiru, sai suka tuntubeshi, amma sai yace ai kyauta suka masa. Daga baya dai ya tambayesu nawane kudin aikinsu i da suka gaya mai dubu dari biyar a...