Monday, February 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gwamnatin tarayya ta baiwa ‘Yan kasar India dubu 11 aikin kamfanin man fetur me albashi me kauri, Kungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN tace bata yadda ba dole a maidasu kasarsu a baiwa ‘yan Najeriya aikin

Gwamnatin tarayya ta baiwa ‘Yan kasar India dubu 11 aikin kamfanin man fetur me albashi me kauri, Kungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN tace bata yadda ba dole a maidasu kasarsu a baiwa ‘yan Najeriya aikin

Duk Labarai
Kungiyar ma'aikatan man fetur ta PENGASSAN ta zargi ma'aikatar kwadago da ma'aikatar harkokin cikin gida da baiwa 'yan kasar India su kusan dubu 11 damar samun aiki a kamfanin harkar man fetur na Sterling Oil Exploration and Energy Production Company Limited. Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace wannan aiki da aka baiwa Indiyawan aikin 'yan Najeriya ne. Dan haka ya bukaci a kwace aikin a baiwa 'yan Najeriya su kuma indiyawan a mayar dasu kasarsu. Yace idan ba'a yi hakan ba, zasu dakatar da ayyukansu sannan zasu shiga gagarumin yajin aiki. Yace ba zai yiyu ana kukan babu aiki a kasa ba a rika dauko 'yan wata kasa da yawa haka ana basu aikin da ya kamata 'yan kasa suke yi ba. Yace dole gwamnati ta zaba ko dai ta goyi bayan '...
Kalli Mutane 10 dake shiga fadar shugaban kasa su ga Tinubu kai tsaye ba tare da shamaki ba, ‘yan Arewa 3 ne kacal a cikinsu

Kalli Mutane 10 dake shiga fadar shugaban kasa su ga Tinubu kai tsaye ba tare da shamaki ba, ‘yan Arewa 3 ne kacal a cikinsu

Duk Labarai
Akwai mutane 10 da basu da shamaki da fadar shugaban kasa inda a koda yaushe zasu iya shiga fadar shugaban kasar su ganshi ba tare da shamaki ba. Wadannan mutane rahoton jaridar Sunnews tace makusanta ne ko kuma ace aminaine na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Gasu kamar haka: Chief Bisi Akande, Jigo a APC Oba Rilwan Akiolu, watau Sarkin Legas Abdullahi Ganduje Shugaban jam'iyyar APC. Orji Uzor Kalu Abdul’aziz Yari: Tsohon gwamnan Zamfara. Oba Sikiru Kayode Adetona Olusegun Osoba Ibrahim Masari Prince Tajudeen Olusi James Ibori
Kalli Bidiyo:Soja ya bace bayan da ya zargi cewa sojojin da aka jiwa rauni a wajan aiki da kudaden Aljihunsu suke kula da kansu a Asibitoci

Kalli Bidiyo:Soja ya bace bayan da ya zargi cewa sojojin da aka jiwa rauni a wajan aiki da kudaden Aljihunsu suke kula da kansu a Asibitoci

Duk Labarai
Wani karamin sojan Najeriya ya bace bayan da ya bayyana cewa sojojin da aka jiwa rauni da kudaden Aljihunsu suke kula da kawunansu ba hukumar sojin ce ke kula dasu ba. Sojan ya bayyana hakanne a wani bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. Yace maganar gaskiya ya ji dadi da aka hana shugaban sojoji Visa zuwa kasar Canada, yace da ba'a hanashi Visar ba da ba za'a san cewa turawanne ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci ba. Yace yana fatan a ci gaba da hana shuwagabannin sojojin Visa dan Asiri ya tonu 'yan Najeriya su san halin da ake ciki game da matsalar tsaro. Kalli Bidiyon lamarin anan
Kalli Wanda shugaba Tinubu ya nada a matsayin me kula da gudanar da jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

Kalli Wanda shugaba Tinubu ya nada a matsayin me kula da gudanar da jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa tsohon shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas mukamin kula da gudanar da jihar rivera bayan da ya dakatar da Gwamna Fubara. A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaban kasar ya dakatar da gwamna Simi Fubara da mataimakinsa da majalisar jihar na tsawon watanni 6 kamin aga abinda hali yayi. Wasu rahotanni sun bayyana cewa, sojoji sun yiwa Gwamna Fubara daurin talala a gidansa tare da iyalinsa.
Falalar Goma na karshe daga bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Falalar Goma na karshe daga bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Duk Labarai
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya kuma shugaban hukumar Hizba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce duk da cewa dukkannin ranaku da dararen watan Ramadan na da falala amma kwanaki 10 na ƙarshen watan sun fita daban. "Goman ƙarshe na da wasu abubuwa guda uku masu muhimmancin kuma wannan ne ma ya sa ake fifita goman ƙarshen a kan goman farko da na tsakiya." In ji Sheikh Daurawa. Allah ya yi rantsuwa da darare 10: Na farko dai Allah ya yi rantsuwa da su inda a cikin Alƙur'ani ya ce Wal Fajr, Wa Layalil A'shar. Malamai sun ce wannan na nuni da kwanakin ƙarshe na Ramadan ko kuma goman farko na watan Zulhijja. Daren Laylatul Qadr ya faɗo a goman ƙarshe: Abu na biyu a cikin wannan watan akwai daren Laylatul Qadr. Idan mutum ya yi dace a daren 21 ko 23 ko ...
Kuma Dai:Akwai yiyuwar shugaba Tinubu zai sake dakatar da wani Gwamnan Nan Najeriya da sake saka dokar Ta baci a jiharsa

Kuma Dai:Akwai yiyuwar shugaba Tinubu zai sake dakatar da wani Gwamnan Nan Najeriya da sake saka dokar Ta baci a jiharsa

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya saka dokar Ta baci a jihar Osun kamar yanda ya saka a jihar Rivers. Sakataren jam'iyyar APC, Ajibola Basiru ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace a jihar Osun an samu dakile ayyukan kananan hukumomi. A jiya ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamnan jihar, Simi Fubara da mataimakinsa da majalisar jihar.
Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakinsa daga mukaminsu

Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakinsa daga mukaminsu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers. Ya bayyana hakane a bayanin da yayi da yammacin yau na Talata inda ya sanar da dakatar da Gwamna Simi Fubara. Hakanan kuma Shugaban kasar ya sanar da dakatar da mataimakin gwamnan na jihar Rivers, Ngozi Odu da duka 'yan majalisun jihar. Dakatarwar an yi ta ne na tsawon watanni 6. An dai samu fasa bututun man fetur a jihar ta Rivers har kusan aau biyu inda shugaba Tinubu yace babu shugaba me hankali da zai ci gaba da kallon wannan abu na faruwa. Shugaban yace ya baiwa sojoji Umarnin su tabbatar an samu tsaron dukiya da lafiyar jama'a a jihar
Kalli Bidiyo: A Sati Idan Na Yi Buge-Bugena Ina Samun Naira Milyan 30, Ka Gaya Min Wane Muƙami Za A Ba Ni A Gwamnati Wanda Zai Rƙe Ni, Cewar Mawaƙi Ali Jita

Kalli Bidiyo: A Sati Idan Na Yi Buge-Bugena Ina Samun Naira Milyan 30, Ka Gaya Min Wane Muƙami Za A Ba Ni A Gwamnati Wanda Zai Rƙe Ni, Cewar Mawaƙi Ali Jita

Duk Labarai
A Sati Idan Na Yi Buge-Bugena Ina Samun Naira Milyan 30, Ka Gaya Min Wane Muƙami Za A Ba Ni A Gwamnati Wanda Zai Rƙe Ni, Cewar Mawaƙi Ali Jita. Kalli Cikakkiyar Hirar da aka yi dashi: https://www.tiktok.com/@freedomradionigeria/video/7482070766842858807?_t=ZM-8un9GUPuTX3&_r=1 Me za ku ce? Daga Abubakar Shehu Dokoki ...
Zan bayyana fitattun mutune bakwai da na taɓa soyayya da su a Najeriya – Bobrisky

Zan bayyana fitattun mutune bakwai da na taɓa soyayya da su a Najeriya – Bobrisky

Duk Labarai
Shahararren ɗan daudun nan, Bobrisky, ya bayyana cewa ya taɓa yin soyayya da fitattun mutane bakwai a Najeriya a cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta. Bobrisky, wanda aka san shi da halayensa masu jan hankali da faɗin albarkacin bakinsa, ya yi wannan bayani ne yayin da yake bayani kan cin amana da suka tilasta masa ficewa daga ƙasar. Jaridar The Nation ta rawaito cewa Bobrisky ya kuma yi alkawarin fallasa sunayen waɗanda ya ke magana a kansu, yana mai kwatanta su da “munafukai” a cikin masana’antar nishadi ta Najeriya. “Lokaci yana zuwa da zan bayyana sunayen fitattun mutune bakwai da na taɓa yin soyayya da su a Najeriya. Lokaci yana zuwa da zan fallasa munafukai a wannan ƙasa”, in ji shi. A cikin bidiyon, Bobrisky ya yi nazari kan suka da ya fuskanta daga wasu ...
Jam’iyyar SDP jam’iyyar karyace kanwar APC ce shiyasa kuka ga ‘yan APC ne kadai ke ta tururuwar shiga cikinta>>Inji Buba Galadima

Jam’iyyar SDP jam’iyyar karyace kanwar APC ce shiyasa kuka ga ‘yan APC ne kadai ke ta tururuwar shiga cikinta>>Inji Buba Galadima

Duk Labarai
Babban dan siyasa, Buba Galadima ya bayyana cewa, jam'iyyar SDP kanwar jam'iyyar APC ce, kuma za'a yi amfani da itace dan murkushe 'yan Adawa. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace idan aka lura yawanci 'yan APC ne ke komawa cikin jam'iyyar. Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne dai ya fara komawa jam'iyyar SDP wanda daga baya aka samu da yawa suka bishi cikin jam'iyyar.