Alamomin mace tana son saurayi
Alamomin mace tana son saurayi suna da yawa, kuma a wannan rubutu, zamu yi kokarin kawo muku su kamar haka:
Da kanta zata rika gaya maka tana sonka: Ba kasafai ake samun irin wannan ba, idan mace na sonka da gaske, zata rika gaya maka tana sonka, kuma zata rika gaya maka hakanne cikin shauki da shagwaba da nuna kaguwa.
Ba ta son rabuwa da kai: Macen dake son saurayinta, a duk sanda suka hadu zaka ganta tana yin kamar ta hadiyeshi, bata son yayi Nesa da ita, tana yawan murmushi, sannan idan zasu rabu, bata jin dadin hakan.
Yawan Kallo: Macen dake son saurayinta sosai, bata gajiya da kallonsa, idan suka hadu zata yi ta kallonshi, idan kuma basa tare, zata yi ta tambayar yaushe zai je tadi, sannan zata yi ta Neman ya tura mata hotunansa.
Zata rika damuwa dashi: Idan mace tana sonk...

