“Idan Aka Kira Ni Naje Aso Villa a Matsayin Uwargidan Shugaban Kasa Ba Zan Je Ba” – Patience Jonathan
Uwargidan tsohon shugaban kasa, Dame Patience Jonathan ta ce idan aka bukaci ta koma fadar shugaban kasa ta yi aiki a matsayin uwargidan shugaban Najeriya, za ta ki ba zata jeba.
A cikin wani faifan bidiyo na Misis Patience, wacce ta yi magana a ranar Juma'a a wurin wani taron jama'a, ta ce " damuwar Najeriya ta yi yawa", tana mai jaddada cewa ta yi kasa da lokacin da take kan mulki.
A cewarta, “Idan kun kira ni yanzu don naje villa, ba zan je wurin ba. Ba zan yi ba. Ba ku ga yadda nake matashiya ba? Damuwar tana da yawa.
“Matsalar Najeriya ta yi yawa. Idan Allah Ya yi nasarar fitar da ku daga cikinta, to ku tsarkake Shi. Ya kai ka can sau ɗaya, me yasa kake son komawa can kuma”?
Dimokuradiyya ta rahoto cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fice daga fadar shugaban ka...