Ƴansanda sun kori ƴandaba da mafarauta daga fadar Kano,ji dalili
Rundunar ƴansanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kori ƴandaba daga fadar sarkin Kano domin daƙile ayyukan dabanci a jihar.
Ƴandaba da mafarauta ne suka kasance suna gadin fadar, wadda Sarki Muhammadu Sanusi II ke zaune a cikin ta yanzu.
Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da PRNigeria cewa matakin ‘yan sandan ya biyo bayan rahotannin sirri da aka samu na kwararowar ƴandaba da ƴantauri wato mafarauta daga ƙananan hukumomi zuwa birnin.
Yanzu haka dai ƴansanda sun karbe iko da fadar ta Gidan Rumfa da ta Nasarawa, inda aka tura jami’ai zuwa wuraren da ke da rauni domin tabbatar da doka da oda.
Yayin da Muhammdu Sanusi II ke ci gaba da zama a Gidan Rumfa, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na zaune ne a fadar sarkin Kano da ke Nasarawa.
A kwanakin baya ne wata kotu da k...