Tuesday, January 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon yanda ‘yan Dàbà ke cin karensu ba babbaka a unguwar Jaen dake Kano

Kano
Mutanen unguwar Jaen a Kano sun koka da ayyukan 'yan daba inda suka nemi daukin Gwamnati kan lamarin. Wani Bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta ya nuna yanda matasan ke cin karensu ba babbaka a unguwar. https://twitter.com/dan_mutangwale/status/1804270313754046935?t=hlC4-9v2DO8CUoCS1X8VOw&s=19 A shekarun baya dai jihar Kano ta yi fama da ayyukan 'yan daba inda suka lafa amma da alama lamarin zai dawo danye.

Hasken fata cikin kankanin lokaci

Kwalliya
Akwai hade-haden abubuwa a gida da zasu kara miki hasken fuska sosai ba tare da kin sayi man shafawa mw tsada ba. Ga abubuwan kamar haka: Ana hada Lemun tsami, Zuma da Madara: Ana saka babban cokali na madara sannan a saka karamin cokali na zuma sai a saka babban cokali na ruwan lemun tsami a dama. Idan suka hadu sosai, sai a shafa a fuska a bari zuwa mintuna 20 a wanke. A ci gaba da yin hakan zuwa sati 1 ko 2, wannan hadi yana sa fuska ta yi fari sosai. Ana kuma yin amfani da ruwan dankalin Turawa. Yanda ake yinshi shine za'a fere dankalin sai a yankashi kanana-kanana a saka a cikin ruwa a rika dauko dankalin aka shafawa a fuska. Ana kuma iya markada dankalin ko a kirbashi, a matse ruwan jikinshi da rariya ko abin tatar koko. Ana iya shafawa a fuska a kwanta das...

Gyaran fuska da zuma

Gyaran Fuska, Kwalliya
Ana amfani da Zuma ta hanyoyi da yawa dan magance matsalar fuska. A wannan rubutu, zamu kawo hanyoyi daban-daban na amfanin Zuma ga fuska. Amfani da Zuma dan saka hasken fata: Ana shafa zuma a fuska dan karawa fuska haske? Zumar ana iya hada ta da ruwa dan rage mata danko. Ana shafawa a fuska na tsawon mintuna 15 zuwa 20 sannan a wanke. Idan kwai tabon ciwo a fuska? Ana iya shafa zuma akan ciwon a barta ta dan dauki lokaci daga baya a wanke. Hakan nasa tabon ciwon ya bace daga fuskar mutum. A yi sau da yawa dan samun sakamako me kyau. Zuma tana kuma wanke dattin fuska tasa ainahin kalar fatar mutum ta bayyana ta hanyar cire matacciyar fatar data like a fuska.
Kalli Takalmin Naira Dubu Dari biyar da ‘yar Cryptocurrency daga Arewa, Barirah ta saka

Kalli Takalmin Naira Dubu Dari biyar da ‘yar Cryptocurrency daga Arewa, Barirah ta saka

Abin Mamaki
KUTURU DA KUDINSA… Mene Ne Aibu Don Barirah Ta Saka Takalmin Kimanin Naira Dubu Dari Biyu A Wankan Sallah? Takalmin da Barirah Musbahu ta saka bai kamata ya zama abin cece ku ce ba a kafofin sada zumunta ba. Duk wanda ya san Barirah Musbahu ya san ta shahara ne wajen shiga gasar "GIVEAWAY" a kafofin sada zumunta, yanzu kuma ta zama cikakkiyar yar crypto (kasuwancin yanar gizo ta zamani). Hakika idan ka san irin makudan Kuɗaɗen da ake samu a hakar crypto bai kamata ka fara tuhumar ta ina ta samu kuɗin sayan wannan takalmin mai tsada a matsayin ta na matashiyar budurwa. Kuma duk wanda ya riki harkar crypto hannun bibbiyu to zaisa abinda yafi haka ma tsada saboda irin kuɗaɗen da ake samu a crypto kuma na halal ga wanda ya kiyaye haram. Barirah Musbahu ba'a iya crypto ta tsay...

Gyaran fuska da kurkur

Gyaran Fuska, Kwalliya
Kurkur na daya daga cikin muhimman abubuwan dake gyara fuska sosai ta yi tas babu kuraje ko duhu ko rauni. A wannan rubutun, zamu kawo muku amfanin da Kurkur kewa fuska da kuma yanda za'a yi amfani dashi. Ana hada Kurkur da dichloromethane, wanda za'a iya samunsa a Kemis da yawa dan maganin duhu da dattin fuska. Hakanan ana hada Kurkur da gyada, Gotu Kola inda suke maganin: Kumburin Fuska. Kaikayin fuska. Da maganin duhu da dattin fuska. Hakanan ana hada Kurkur da Gotu Kola da Rosemary inda suke maganin alamun tsufa dake bayyana a fuska. Dan samun sakamako me kyau a yi sati 4 ana amfani dasu. Hakanan ana amfani da Kurkur wajan gyara tabon ciwo a fuska. A takaice idan duk ba'a samu abubuwan da muka bayyana a sama ba, ana hada Kurkur da Yoghurt ko zuma a kwaba a sh...

Gyaran fuska da kwai

Gyaran Fuska, Kwalliya
Ana amfani da kwai wajan gyaran fuska sosai dan magance matsalolin da kan iya shafar fuska. Ga hanyoyin da ake amfani da kwan kamar haka: Ana fasa kwan a cire kwaiduwar a bar ruwan kwan kawai sai a hada da zuma, da ruwan lemun tsami ai ta bugawa har sai sun hadu. Idan ya hadu sosai sai a wanke fuska da ruwan dumi. A fara shafawa a hannu adan barshi zuwa mintuna biyar, idan ba'a ga wata matsala ba, daga nan sai a shafa a fuska,dalilin yin hakan shine wasu yana musu reaction. A barshi ya kai mintuna 10 zuwa 15 a fuska? Daga nan sai a wanke. Ana iya yin hakan sau 3 a mako. Wannan hadi yana sa fatar fuska ta yi laushi ta yi kyau sosai? Yana maganin kurajen fuska da kawar da tattarewar fuska da kuma maganin tsufan fuska. Sannan kuma ana yin hadin Ruwan kwai, Shima a cire...
Kalli Bidiyo: Yanda matasa suka yi mummunan hàdàri a Jalingo saboda tukun ganganci

Kalli Bidiyo: Yanda matasa suka yi mummunan hàdàri a Jalingo saboda tukun ganganci

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wasu matasa da suke tukin ganganci a Jalingo na jihar tarabawa sun yi hadari inda motarsu ta juya. Bidiyon faruwar lamarin ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda akai ta musu Allah wadai, wasu kuma na musu jaje. Saidai babu wanda ya rasu amma dai an ji raunika.