Ciwon zuciya ya danganta da irin zuciyar, akwaishi kala-kala.
Dan haka bari mu bayyana alamomin ciwon zuciya daban-daban.
Akwai wanda ake kira da Coronary artery disease: Wannan kalar ciwon zuciya ne dake taba hanyoyin dake baiwa zuciyar jini.
Wannan kalar ciwon zuciya shine wanda yafi kama mutane kuma yakan kai ga Bugawar Zuciya da ke iya kaiwa ga mutuwa, Yakan kuma kai ga ciwon kirji, ko shanyewar rabin jiki.
Alamomin wannan ciwon zuciya ya banbanta a tsakanin mata da maza, misali, idan ya kama maza, zasu iya fuskantar ciwon kirji, yayin da idan ya kama mata, zasu iya fuskar Ciwon kirjin da karin wasu matsaloli da suka hada da numfashi sama-sama, da yawan zazzabi da safe da kuma matsananciyar kasala.
Ga dai alamomin ciwon zuciya na Coronary artery disease dake damun maza d...