Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia
Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Task Force Tactical Patrol Squad sun kai wani samame a wani sansanin horas da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da takwararta ta ESN a unguwar Ihechiowa na ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar Abia.
A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kutsawa tare da tarwatsa sansanin da kuma lalata dukkan na’urorin horas da mayaƙan da kuma kayayyakin da aka samu a wurin.
Rundunar sojin ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X.
Cikin wata sanarwa da da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce samamen da sojojinta suka kai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin IPOB da ESN ke yi, waɗanda ke da alaka da kalubalen tsaro da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan ‘yan ƙasa da ...