Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji
Gwamnatin jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta saka ladan naira miliyan 25 ga duk mutumin da ya bayar da bayanan da za su taimaka a kama mutanen da suka kashe sojoji a jihar.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Okey Kanu ya fitar, gwamnatin jihar ta aike da sakon ta'aziyya ga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja kan faruwar lamarin.
A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka afka wa sojoji a wani shingen bincike a mahadar Obikabia da ke yankin tsaunin Ogbor, tare da kona motar aikinsu.
Rahotonni sun ce wasu sojojin sun samu tsallake rijiya da baya a harin.
“Domin samun saukin kama maharan, gwamnati ta yi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su,'' in ji s...