Friday, December 5
Shadow

Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa

Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa.

Gwamnatin Jihar Adamawa ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai cewa ta cire tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga sarautar Wazirin Adamawa.

A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa da ke bayyana cewa mutanen da ke masarautar su ne kaɗai ke da hakkin naɗa basarake da mambobin majalisar masarauta.

Wannan sabon tsarin ya sa kafafen yada labarai da dama suka fassara cewa an cire Atiku daga matsayin Wazirin Adamawa.

Amma a wani taron manema labarai da aka gudanar a jiya Laraba, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare na Jihar Adamawa, Iliya James, ya bayyana cewa wannan sabon tsarin bai cire kowa daga mukaminsa ba.

Karanta Wannan  Duk ofis din Abuja na shigesu in banda 'yan kadan, kuma ba kirana ake ba, ni ke zuwa neman na kaina>>Mansurah Isah

Ya kuma ƙara da cewa duk wasu sabbin shirye-shirye da gyare-gyare da ake yi a harkar gargajiya da sarauta ba don a muzugunawa kowa a ke yi ba sai dan karfafa al’ada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *