Thursday, June 5
Shadow

Ba gaskiya bane cewa bama ciyar da masu laifi abinci me kyau, Abinci me rai da lafiya muke basu>>Hukumar Gidajen Gyara Hali ta Najeriya

Hukumar Gidajen Gyara Hali ta Najeriya ta musanta ikirarin dake cewa, tana ciyar da masu laifi abinci da bashi da sinadaran gina jiki.

Kakakin hukumar, Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan.

Yace Rahoton ba gaskiya bane, suna bin doka da oda wajan ciyar da masu laifi abinci kamar yanda aka tanadar. Yace kuma kwanannan gwamnati ta kara yawan kudin ciyar da kowane me laifi zuwa Naira ₦1,125 a kullun.

Yace ba a boye suke baiwa masu laifi abinci ba, akwai kungiyoyin kare hakkin al’umma da hukumomi na cikin gida da kasashen waje dake saka ido kan yanda ake ciyar da masu laifin amma basu bayar da wani korafi kan yanda ake ciyar da masu laifin ba

Karanta Wannan  Jam'iyyar NNPP ta yi bayani dalla-dalla kan komawar Kwankwaso APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *