Friday, December 5
Shadow

Ba kamar yanda ake cewa mun Kàshè ‘yan sa kai da yawa ba a Zamfara, Guda biyu ne kawai suka mùtù bayan jirgin saman mu yayi kuskuren jefa musu Bàm da tunanin cewa ‘yan Bìndìgà ne>>Hukumar Sojojin Najeriya

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai hare-hare ta sama a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar, tana mai cewa dakarun sa-kai biyu sun rasu yayin da take harar ‘yanfashin daji.

A jiya Litinin ne mazauna ƙaramar hukumar Maru suka shaida wa BBC Hausa cewa jirgin yaƙin sojin ya kashe ‘yan sa-kai, yayin da ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mayaƙa 20 aka kashe a lokacin da suke bin sawun ‘yanbindigar da suka kai musu hari da sace wasu mutane.

Kakakin rundunar Ehimen Ejodame ya ce hare-haren da suka kai bayan samun bayanan sirri sun yi sanadiyyar kashe ‘yanbindigar 20.

Karanta Wannan  Matatar Ɗangote ta sake rage farashin man fetur

“A martanin da muka mayar cikin gaggawa ranar 31 ga watan Mayu, dakarunmu sun kashe sama da ‘yanta’adda 20 tare da lalata babura fiye da 21,” a cewarsa yayin wani taron manema labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Abin takaici, yayin wannan aiki ne kuma ‘yan sa-kai biyu suka rasa rayukansu kuma wasu biyu suka ji raunuka. Rundunarmu ba ta ji daɗin abin da ya faru ba kan waɗannan jajirtattun mutane kuma muna aiki da hukumomin yankin domin kare rayukan al’umma.”

Sai dai har yanzu mazauna yankin na cewa mutanen da suka mutu a hare-haren kuskuren sun zarta mutum biyu kamar yadda rundunar ta bayyana.

Karanta Wannan  Wahala ta yi yawa, A tausayawa Talakawa>>Tsohon Shugaban kasa,Abdulsalam Abubakar ya roki Gwammati

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *