Monday, December 16
Shadow

Ba mu ƙara kuɗin da muke kashewa a tallafin man fetur ba – NNPCL

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya musanta rahotannin da ke cewa ya kara kudin tallafin man fetur da sama da naira tiriliyan uku a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye, ya jaddada cewa an tabbatar da ikirarin tallafin da kamfanin ya bayar, tare da mika dukkan bayanan da suka dace ga hukumomin da suka dace.

Ya kuma bayyana cewa kamfanin na NNPCL bai san wani shiri na tantance asusun ajiyarsa ba, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai na farko suka nuna.

“NNPCL ta lura da wani rahoto a wani sashe na kafafen yada labarai da ke zargin cewa ta kara kudin tallafin da naira triliyan 3.3,” in ji Soneye.

Karanta Wannan  Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote

“NNPCL tana gudanar da kasuwancinta ne cikin gaskiya bisa kyawawan halaye na ƙasashen duniya, kuma ba ta taɓa ƙara wani kuɗin tallafi man fetur ba ga Gwamnatin Tarayya.” in ji sanarwar

“Duk da’awar tallafin da aka yi a baya ana iya tabbatar da su, tare da rubuce-rubuce da takardu da aka aika ga hukumomin da abin ya shafa.” Sanarwar ta ƙara haske.

Kamfanin ya kuma jaddada ƙudirinsa na yin aiki bisa tsarin kasuwanci a ƙarƙashin dokar masana’antar man fetur tare da bayyana cewa zai bijire wa duk wani yunƙuri na siyasantar da batun tallafin man fetur.

Sanarwar ta ƙara da cewa “NNPCL ta gayyato masu binciken kuɗi na waje don yin bitar littattafanta a lokuta da dama.”

Karanta Wannan  Ko da matatar Dangote ta fara tace man fetur ba lallai farashinsa ya sauko ba>>Inji Masana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *