Wednesday, January 15
Shadow

Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma’aikata mafi karanci a ƙasar.

Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000.

A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.

Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu yace yana sane da halin matsin da 'yan Najeriya ke ciki inda ya bayyana matakan kawo sauki da zai dauka

Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeyanju, ya ce babu wata yarjejeniya da kwamitin bangarori uku suka cimma kan batun mafi karancin albashi na kasa a lokacin da aka kammala tattaunawa a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni, 2024.

Ya ce, “Har yanzu bukatarmu ta mafi ƙarancin albashin ma’aikata na nan a kan naira 250,000, kuma ba a ba mu wasu kwararan dalilai na sauya wannan abu da muka yanke ba”.

Kungiyar ta NLC ta ce ya zama wajibi ta “jawo hankalin shugaba Tinubu da ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki su sani domin da alama waɗanda suka yi masa bayanin sakamakon tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin uku ba su fada masa hakikanin halin da ake ciki ba”.

Karanta Wannan  El-Rufa'i ya maka majalisar dokokin Kaduna a kotu

Sanarwar ta kara da cewa: “Duk da cewa shugaban kasa ya yi cikakken bayanin wasu sassan tarihin tafiyar dimokuradiyya, a bayyane yake cewa ba a yi masa cikakken bayani game da sakamakon tattaunawar mafi ƙarancin albashi ba.

Ƙungiyar ta ce babu wata yarjejeniya kuma dole ne ta fahimtar da shugaban kasa da ’yan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki na kasa kan hakan.

Al’ummar Najeriya dai sun yi tsammanin ko shugaban ƙasar zai faɗi matsayarsa game da sabon ƙarancin albashin ma’aikata a Najeriyar, wanda aka gaza cimma matsaya tsakanin ƙungiyar ƙwadago da ɓangaren gwamnati a tattaunawar da aka kammala cikin makon da ya gabata.

Karanta Wannan  Lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na gwamnan Kaduna an cire Naira Biliyan 423 daga asusun bankin jihar ba tare da yin wani aiki da kudin ba>>Majalisar Jihar

Yayin da ƙungiyar ƙwadago ta dage kan naira 250,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, ɓangaren gwamnati da ƴan kasuwa sun kafe ne a kan naira 62,000.

Yanzu haka dai ana jiran matakin da ƙungiyar ƙadagon za ta ɗauka bayan ƙarewar wa’adin da ta bayar na samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar, wanda yana cikin sharaɗin da ta gindaya gabanin janye yajin aikin da ta fara a ranar Litinin ɗin makon da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *