
Dan Ministan harkokin kasashen waje, Adam Tuggar ya musanta rahoton dake cewa mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Jatau ya mari babansa.
Rahotanni dai sun bayyana cewa dan Gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed ne ya yada wannan labari a shafinsa na sada zumunta.
Da yake mayar da martani, Adam Tuggar ya bayyana Shamsuddeen a matsayin wanda bashi da tarbiyya wanda kuma shi da babansa sun yi zaman gidan yari kamin baban nasa ya zama Gwamna.
Sannan yace wannan dabi’a da yake nunawa a wajen mahaifinsa ya gajeta.
Yace shi baya shiga irin wannan lamari amma tunda an taba babansa, dole ya fito ya kareshi.
Yace Shamsuddeen Ya saba yiwa manyan mutane irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar rashin kunya saboda kawai su na da banbancin ra’ayi da mahaifinsa.
Yace shi kakansa yayi sanata a jamhuriya ta biyu yace shi kuma a wancan lokacin ina kakansa yake? Waye shi, wa ya sanshi sannan wane ci gaba ya kawowa jihar Bauchi?.
Yace kamata yayi baban Shamsuddeen ya mayar da hankali wajan aikin dake gabansa na gudanar da gwamnatin jihar Bauchi.