Friday, December 5
Shadow

Ba zaka bata mana suna ba, Ka kawo shaidar cewa, Sai an biya Naira Miliyan 3 ake gabatar da kudirin doka a majalisa ko mu hukunta ka>>Majalisar Wakilai ga dan majalisa, Ibrahim Usman Auyo

Majalisar wakilai ta bukaci dan majalisar daga jihar Jigawa me wakilar Hadejia, Auyo, da Kafin Hausa, Ibrahim Usman Auyo ya fito ya kawo shaidar cewa sai an biya kudi ake gabatar da kudirin doka a majalisar.

Dan majalisar dai yayi wannan ikirarin ne a yayin ganawa da mutanen mazabarsa.

Inda yace Ana biyan daga Naira Miliyan daya zuwa 3 kamin gabatar da kudirin doka a majalisar.

Saidai a martanin majalisar ta bakin me magana da yawunta, Akin Rotimi tace ba zata bari a bata mata suna ba, wannan ikirari na dan majalisa, Ibrahim Usman na da girma kuma zata bincikeshi ya bata hujjarsa.

Tace amma idan bai bayar da wata hujja ba, zata gabatar dashi a gaban kwamitin da’a na majalisar.

Karanta Wannan  Na Gano cewa: Yawanci mazan Kano basa iya ciyar da matansu, sannan ana yiwa yara mata auren wuri>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *